Da Dumi-Dumi

Zan Hada Kai Da ‘Yan kasuwa Domin Samar Da Managarta Shirye-shiryen Farfado Da Kasuwanci A Kasuwar Singa – Hon Kwasamgwami

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar ‘Yan kasuwar Singa karkashin Kungiyar (AMATA) ta jaddada goyan bayanta na tabbatar da an kawo managartan shirye-shiryen da za su bunkasa harkokin ‘Yan kasuwar  ta tsayar da Muntari Mohammed Liti Kwasamgwami Shugaba na kasuwar a zaben dake tafe.

Sakataren Kungiyar na AMATA Alh. Balarabe ne ya bayyana hakan a lokacin da yake kira ga matasa da ‘Yan kasuwar da su marawa Mohammed Liti domin kawo sauyi da ci gaba mai dorewa a cikin kasuwar ta Singa.

Yace, lokaci yayi da za’a sanya matasa masu kishi wajen ganin sun Shugabanci Kungiyar kasuwar gaba dayanta domin al’umma su san ana yi da su musamman wajen kawo taimako daga Gwamanati mai ci a halin yanzu.

A jawabinsa, Dantakarar Shugabancin Kungiyar tun da farko ya sha alwashin yin aiki kafada da kafada da manyan ‘Yan kasuwa da kanana da matasa da sauran Al’ummar Singa ta yadda za’a farfado da ita kamar lokutan da suka gabata.

Muntari Mohammed Liti Kwasamgwami, ya bayyana cewa, akwai aikace aikace da ya sanya a gaba da zarar ya samu darewa wannan Kujera ta Shugabancin Kungiyar kasuwar ta Singa.

Yace, daga cikin abubuwan da zai fara yi, akwai samar da magudanan ruwa domin kaucewa afkuwar ambaliya da inganta rayuwar matasa, musamman leburori da kananan ‘Yan kasuwa wadanda ke bukatar tallafin jari daga hannun Gwamnatin jihar Kano.

Mohammed Liti Kwasamgwami, ya kara da cewa, akwai samar da tsaro da kare martabar dukkannin ‘Yan kasuwar da suke fuskantar matsaloli daga wasu hukumomi babu gaira ba dalili ta hanyar cin mutuncinsu ba tare da an tuntubi hukumar gudanarwar kasuwa ba.

Dan takarar yace, za kuma su marawa yunkurin Gwamnatin jihar Kano baya na farfado da tattalin arzikin kasuwanci ta hanyar zamanantar da al’amura yadda suka kamata.

Ya jaddada cewa, Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa, Gwamnatinsa tana da tsare-tsare musu yawa ga al’ummar jihar musamman ‘Yan kasuwa karkashin jagorancin ma’aikatar kasuwanci dahke jihar.

Yace, Kwamishinan Ma’aikatar Kasuwanci da Ciniki Abbas Sani Abbas, Dan kasuwa ne daya san halin da ‘Yan kasuwa suke ciki, kuma ya bayyana cewa, zai hada kai da kungiyoyin ‘Yan kasuwa domin ciyar da kasuwanci gaba a fadin jihar Kano da ma kasa baki daya.

Mohammed Liti yace, yawan kiraye-kirayen da al’ummar Singa suke yi masa a matsayin Dan kungiyar Kwankwasiyya da Kungiyar (AMATA) ya ga dacewar ya fito domin bayar da tasa gudunmawar ta hanyar shugabantar al’umma da ma kasuwar singa Dingurungun.

Haka zalika, Dan takarar ya nemi hadin kan al’umma da suke kasuwanci manya da Dattijai da matasa maza da mata da bashi hadin kan da ya kamata domin ganin an samu nasarar kawo sauyi mai nagarta ta kowanne fanni na kasuwar ta Singa duba da kasancewar jihar Kano cibiya ce ta kasuwanci a fadin kasar nan da ma kasashen ketare.

 

Leave a Comment