Ilimi

Zamu Zo Da Sabbin Tsare-tsare Ga Shugabancin Daliban Kano -Getso

Written by Pyramid FM Kano

Daga: KABIR GETSO

Shugaban Hukumar bada tallafin karatu (Kano state Scholarships Board)
Kabiru Getso Haruna ya bayyanna cewa zasu zo da sabbin tsare-tsare ga shugabancin Kungiyar Daliban Kano domin dawo da martabar tsarin shugabanci.

Kabiru Getso ya bayyanna hakan ne lokacin da shugabncin Daliban Jami’ar Bayero ‘Yan Asalin Garin Getso suka kai mashi ziyara a Ofishinsa, yace a gwamnatin baya kunshin shugabancin ya samu matsaloli na nuna bangaranci na siyasa wanda hakan ya saba da tsari da dokokin kungiyar.

Kabir Getso ya kuma yabawa Daliban jihar Kano bisa nuna da’a da dattako ga Gwamnatin Jihar Kano, inda yace nan bada dadewa ba Gwamnatin Jihar Kano zata biyawa dukkanin Daliban Jihar Kano dake karatu a Jami’ar ta Bayero kudin tallafin.

Shima a nasa jawabin, Shugaban kungiyar Daliban BUK na ‘yan asalin Garin na Getso Comrade Shehu Mansur ya bayyanna godiya da yabawa bisa yadda Shugaban Hukumar ya karbe su hannu bibiyu tare da bayyanna makasudin kawo masa wannan ziyara ta musamman.

Kabiru Getso ya karbi dukkanin rokon da aka gabatar masa tare da shan alwashin cewa Gwamnatin Kano zatayi duk mai yiwuwa wajen ganin Dalibai sun samu tagomashi kala-kala, kamar yadda tuni shiri yayi nisa wajen shirin tura Dalibai Kasar wajen su kimanin dubu da daya.

Leave a Comment