Labaran Jiha

Zamu yi aiki Tukuru Da ‘Yan Jaridu Wajen Tallata Manufofin Gwamnati

Written by Admin

Gwamnatin jihar Kano zata yi aiki kafada da kafada da yan jaridu domin bunkasa manufofi da kuma aiyukan kananan hukumomi a fadin jihar Kano.

Babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomin jihar nan Ibrahim Kabara ne ya sanar da hakan a lokacin da a yarin ‘yan jaridu na ofishin mataimakin Gwamna suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa dake nan Kano.

Alhaji Ibrahim Kabara ya bayyana farin cikinsa bisa wannan ziyarar da aka kawo masa. Inda yace, babu wata gwamnati da tasan abin da take yi da zata yi wasa da ‘yan jaridu, kasancewar sune suke tallata manufofin gwamnati dama irin aiyukan da take yi domin cigaban al’ummar jiharta.

Ya kuma yabawa a yarin ‘yan jaridun musammam ta fuskar muna kokarin su wajen gano matsala a gwamnatance ta yadda da zarar gwamna taji zata dinke barakar nan take.

Ya kara da cewar, ‘yan jaridu sune idanun gwamnati kasancewar kananan hukumomin jihar Kano 44 da suke gudanar da aikinsu ta dalilin ‘yan jaridu ne al’ummar zasu san ana gudanar dasu.

Don haka ya basu tabbacin hadin kai da goyon baya dari bisa dari wajen yin tafiya da kuma aiki tare.

Shima anasa bangaren, shugaban a yarin ‘yan jaridu na ofishin mataimakin Gwamna Najib Lawan Dambazau yace, sun kawo ziyarar ne domin taya shi murnar samun kujerar sa da kuma sanin yadda ma’aikatar ke gudanar da aikinta.

Leave a Comment