Labaran Jiha

Zamu Wayar Da Kan Mutane Game Da Ayyukan Raya Kasa na Ganduje — Bashir Rufa’i

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Kamal Yakubu Ali

Sabon Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje a ma’aikatar yada labarai Bashir Rufa’i Lawan a ya bayyana cewa zasu cigaba da wayar da kan mutane a game da ayyukan da Ganduje ke gudanarwa a loko da sako dake fadin jahir Kano.

Bashir Rufa’i Lawan a ya bayyana haka ne a yayin da yake kama aiki a matasa yin babban mataimaki na musamman ga gwamna a ma’aikatar yada labarai Mai taken Kano a yau.

Ya ce a shirye yake wajen yada ayyukan da gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje yake gudanarwa domin cigaban alumma loko da sako dake fadin jihar nan, inda ya ce zai Hada hannu da kafafen yada labarai na gaida da waje domin sanar da allumma ayyukan cigaba da Gwamnatin ganduje ke gudanarwa a fadin jahar Kano.

Ku karanta: An karrama Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin Kano

Shima a nasa jawabin, Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya bayyana Honarabil Bashir Rufa’i Lawan a matsayin jajirtacce matashi wanda ya jajirce wajen hidimtawa alumma, inda ya bukace shi da yayi amfani da kwarewar da yake da ita wajen samar da cigaba da wayar da kan matasa, kasancewar matasa sune kashin bayan cigaban kowacce alumma.

Muhammad Garba ya bukaci daukacin yayan jamiyyar APC dake karamar hukumar Birni dasu kara damara, da kuma hadin kai domin samun Nasarar jamiyyar APC a zabuka dake Tafe na shekarar 2023

Alumma da damane suka raka Sabon babban mataimakin domin sheda shiga office wadanda suka hadarda shugaban karamar hukumar birni Faizu Alfindiki da shugabannin jamiyya APC na Karamar hukumar Birni Sani fara sharada da da sauran mihimman mutane.

Leave a Comment