Labaran Kasa Tattalin Arziki

Zamu Tabbatar Da Karbo Kaso 13 cikin 100 Na Ma’adanan Da Ake Haka a Kano — Adamu Fanda

Written by Pyramid FM Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata tabbatar da karbo kaso 13 cikin 100 na ma’adanan da ake haka a nan Kano daga gwamnatin tarayya domin gudanar da ayyukan cigaba.

Kwamishinan Kudi na jihar Kano Adamu Abdu Fanda ne ya bayyana hakan lokacin da jami’an hukumar tattarawa da kuma raba arzikin kasa ta gwamnatin tarayya suka kawo ziyara a nan Kano domin bibiyar guraren da ake hako ma’adanai, da yadda aikin yake gudana.

Kwamishinan wanda babban sakataren ma’aikatar Dakta Lawan Shehu Abdulwahab ya wakilta ya ce dukkan matsalolin da aka gano a guraren hakar ma’adanan dama garurun da ake aikin za’a dauki matakin da ya da ce domin cigaban aikin.

“Ziyarar ta wannan lokacin ta mayar da hankali ganin irin cigaban da aka samu a fara aikin hako ma’adanai da aka fara a shekarar 2016 sakamakon wani shiri na Gwamnatin Tarayya na bunkasa tattalin arzikin da hanyoyin kudin shiga”, Dr Abdulwahab.

Ku karanta: Muna Rokon Gwamnatin Kano ta Gyara Titin Railway zuwa Audu Bako — Mamuda Zango-Kabo

“Munje karamar Hukumar Sumaila garin Rimi inda ake hakar maaidanai na Gwal, Akwai namu da mutanen mu suke yi akwai Kuma wanda wani ya hada Kai da mutanen China”. “Sannan munje da su garin Fanisau inda kuma muka ga kamfanin fasa dutse na jihar Kano”, inji Abdulwahab.

Ya ce “Munje da su Garin Rimin-gado inda ake fasa Dutse, sannan Munje da su karamar hukumar Shanono, wani guri da aka fara hakar maadanai shima”.

“Abin da ake so ayi shine a tattaro mutanen nan a nuna musu cewa suna da muhimmanci a cigaban tattalin arzikin jihar Kano dama Nigeria”, inji Shi.

Ya ce a ranar karshe na taron sun kira dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin hakar ma’adanai domin tattaunawa tare da daukar matakan da suka dace.

A jawabinsa, shugaban ayarin kuma Daraktan dake kula da ingancin maadanai na hukumar Tanimu Adamu Aliyu ya ce zasu tabbatar da yin aiki kafada-da-kafada da gwamnatin jihar Kano domin daukar matakan da suka dace ciki harda ganin cewa jihar ta Kano na samun kaso 13 ciki 100 da kudade da ake samu a hakar maadanai.

Ku karanta: Nadin Lamin Sani Kwamishina Abu Ne Da Ya Dace — Samarin Tijjaniyya

“Dama abun da ya kawo mu shine mu tabbatar da yadda harkokin kudin shiga yake na Gwamnatin Tarayya da kuma yadda ake hakar ma’adanai a nan Kano, Kuma abin ya Bada sha’awa bisa yadda kan mutane ya waye kan yadda za’a halo ma’adanai”, inji Tanimu.

A yayin taron masu aikin hakan ma’adanan sun koka kan yadda ake bawa mutum fiye da daya lasisin hakar maadanai a guri daya.

Leave a Comment