Labaran Jiha Labaran Kasa

Zamu Tabbatar Da Hadin Kan Kiristoci Hausawa ‘Yan Asalin Jihar Kano — Saratu Godia

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Mustapha Gambo Muhammad

Kungiyar Hausawa Mabiya Addinin Kirista ‘yan Asalin Jihar Kano ta ce zata yi duk Mai yuwuwa da nufin hada kan ‘ya’yan kungiyar domin yin magana da murya daya da nufin Samar da cigaban ‘ya’yan ta.

Shugabar Kungiyar Saratu Godia ce ta bayyana hakan a tattaunawarta da manema labarai a nan Kano.

Misis Godia ta ce an shirya taron ne domin hada kan ‘ya’yan kungiyar da nufin yin magana daya a dukkan matakai da kuma samar da tsare-tsare da zasu kawo cigaban ‘ya’yan ta.

Ta ce lokacin zabe yana karatowa hakan ne ya sa zasu tabbatar da hada kan ‘ya’yan kungiyar domin sanin Junan su da kuma zabar Mutumin da ya cancanta a zabe Mai zuwa na 2023.

“Min hada taron ne domin sanin Junan mu, Kowanne da ka gani ya fito daga wata Karamar hukuma, mun zabo mutane biyu-biyu daga kananan hukumomin Kano 44 domin mu hada Kai musamman yanzu ga zabe yana karatowa hakan zai bamu damar Mutumin da ya cancanta”, inji Godia.

Ta ce “Kiran da nake da Kiristoci ‘Yan Asalin Jihar Kano shine wannan ya kamata mu fito mu gabatar da kanmu, domin bamu da gurin da zamu je, ku ruwa ko rana ko zabi me Mai zai faru bamu da wata jihar, bamu da wani garin sai Kano domin mu ‘yan Asalin Jihar Kano ne Kuma a nan aka haife mu”.

Shugabar ta Kara da cewa “manufar shine ne mu tattaru, mu bawa juna shawara, mu Fadi damuwowin da muke da shi, mu Kuma gabatar da kanmu ga hukumomin da suka da ce cewa mune hausawa Kiristoci ‘Yan Asalin Jihar Kano”.

Ku karanta: Majalisar Dokokin Kano ta Amince Da Sauya Sunan KUST Zuwa Jami’ar Kimiyya ta Dangote

A jawabinsa, sakataren kungiyar Sama’ila Dan-tine ya ce taron ya mayar da hankali domin samun ‘yancin Hauwasa Kiristoci ‘Yan Asalin Jihar Kano kamar yadda kowa ya ke da shi a nan Kano.

Sama’ila Dan-tine ya ce suna kuma wayar da kan ‘ya’yan kungiyar yadda zasu gudanar da al’amuransu musamman a zaben shekarar 2023 da ke tafe.

Yayi fatan dukkan Mabiya Addinin Kirista Kuma Hausawa a nan Kano zasu bayyana kansu a duk jam’iyar da su ke domin bada gudun mowar wacce suma zasu amfana idan anyi nasara.

Leave a Comment