Ilimi Kimiyya Labaran Jiha

Zamu Sauya Tsarin Koyar da Sana’o’i da NUC ta zo da shi Don Samarwa Matasa Aiki — Farfesa Kurawa

Written by Pyramid FM Kano

Shugaban jami’ar Yusuf Maitama Sule a nan Kano Farfesa Muktar Atiku Kurawa ya ce zasu sauya Tsarin ilimin koyar da sana’o’i da hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta zo da shi domin aiwatar da sana’o’in a aikace da nufin samarwa Matasa da dalibai ayyukan yi.

Farfesa Muktar Atiku Kurawa ya bayyana hakan ne a taron karawa juna da hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta Tarayya (NITDA) ta shirya hadin gwiwa da ofishin Mai taimakawa gwamnan Kano a harkokin fasaha (ICT) da ya gudana a jami’ar Yusuf Maitama Sule dake nan Kano.

Ya ce hukumar ta zo da shirin ne domin koyawa dalibai dabarun koyon sana’o’i da nufin dogaro da Kai da kuma bunkasa tattalin arzikin matasa da kuma jihar Kano.

Shugaban ya ce taron wanda aka shirya da nufin nunawa Matasa dabaru da kuma hanyoyi amfani da kafofin sada zumunta na zamani kamar su Facebook da Whatsapp da Twitter da Instagram da YouTube da ma sauran manhajoji ya zo dai-dai a lokacin da ake bukatarsa la’akari da yadda dukkan masata ke amfani da kafofin sada zumunta wajen tattaunawa kawai da kuma yada wasu labaran wadanda ba za su amfane su ba.

Farfesa Kurawa yayi fatan mahalarta taron za su yi amfani da taron na kwanaki biyu domin samun kwarewa da dabarun da za su taimaka musu wajen cigaban rayuwar su.

Ku karanta: Zamu Kashe Miliyan 70 a Fadada Magudanan ruwan Shataletalen Baban Gwari — Kabiru Getso

“Daga abin da na gani, ina da tabbacin cewa mahalarta taron za su amfana so sai, la’akari da yadda ake nuna musu hanyoyi yin amfani da ‘Social Media’ domin cigaban su, maimakon su rika ‘chatting’ da ‘Posting’ abubuwan da basu da ce ba”, inji Kurawa.

A jawabinsa, mai taimakawa gwamnan Kano kan harkokin sadarwa da aiwatar da harkokin gwamnatin ta amfani da sadarwa Injiniya Mustapha Ibrahim ya ce an shirya taron ne domin koyawa Matasa hanyoyin amfani da kafofin sada zumunta wajen bunkasa kasuwanci su da samun kudaden shiga.

Ya ce gwamnati ba zata ta iya bawa kowa aiki ba, a don haka akwai bukatar Matasa su yi kokarin samawa kansu aiki ta hanyar amfani da kafofin sada zumunta wajen bunkasa tattalin arzikin kansu da kansu.

“Akwai Bincike da akayi ya nuna cewa a duk Africa Nigeria ce ke kan gaba a Matasa wanda suka tashi daga shekaru 18 zuwa 35 kuma mafi yawancin su Arewacin Nigeria kuma mafi yawancin su sun fito ne daga jihar Kano, dalilin da yasa kenan muka ga dacewar mu shirya taron domin wayar da kan su yadda za su yi amfani da kafofin sada zumunta don cigaban kansu”, inji Mustapha.

Ya ce “An koyawa matasan yadda za su koma yin harkokin kasuwanci ta internet da ba tare da kaga mutum ido-da-ido ba”, “yanzu duniya ta yi cigaban dole sai ka fadada tunanin ka ta amfani da internet domin cigaban al’umma”.

Ku karanta: Kotu Ta Ki Amincewa A Mayar Da Shari’ar Abduljabbar Abuja

Daga bisani yayi fatan Matasan za su yi amfani a wayoyin da suke da shi domin cigaban rayuwar su Maimakon zama Yan jagaliyar siyasa.

Wasu daga cikin mahalarta taron da suka hada da Muktar Bako Getso da Aminu Dan-malam sun bayyana farin cikin su dagane da halartar taron, su na masu cewa taron yazo dai-dai a lokacin da suke bukatar sa la’akari da yadda zai taimaka musu a cigaban harkokin kasuwanci da ma bunkasa rayuwar su.

Leave a Comment