Da Dumi-Dumi Kasuwanci

Zamu Nemowa ‘Yan Kasuwarmu Tallafi Daga Gwamnatoci

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar masu sana’ar amfanin gona ta jihar Kano ta jaddada kudurinta na samarwa da ‘ya ‘yanta tallafin gudanar da kasuwanci daga gwamnatoci a matakai daban daban dake fadin kasar nan.

Shugaban harkokin matasa na kungiyar kasuwar ‘Yan gyada anan Kano dake Tafawa Balewa Road Alh. Aminu Inuwa ne ya jaddada hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da shigowar lokutan kaka wanda kungiyar ta gudanar.

Yace, kungiyar kasuwar ‘yan gyada ba za ta gajiya ba wajen nemowa ‘ya ‘yanta abubuwan da za su bunkasa harkokin kasuwancinsu na yau da kullum.

Aminu Inuwa yace, kungiyar ‘yan gyada dake Tafawa Balewa ta cike dukkannin wasu sharuddan da aka bukaci da ta cikesu a lokacin gwamnatin da ta gabata amma har ya zuwa yanzu, babu wani tallafin kasuwanci da ya shigo hannunta.

Shugaban ya bayyana cewa, yana da kyakykyawan yakini akan wannan gwamnati mai ci cewa ba za ta yi kasa a gwuiwa ba wajen bibiyar irin wadan nan tallafe tallafe da aka tafi ba’a biyasu ba.

A don haka yake kira ga gwamnatoci a matakai daban daban, da su taimakawa kungiyoyin da suka yi rijista domin neman tallafin bunkasa harkokin kasuwanci a fadin jihar Kano da ma kasa baki daya.

Aminu Inuwa ya kara da cewa, ‘Yan kasuwar da suke gudanar da kasuwanci gyada da waken suya da sauran kayayyakin amfanin gona, suna mutukar bukatar taimakon gwamnati tun daga jiha zuwa kasa baki daya kamar yadda aka taimakawa kungiyoyi na noman alkama da dai sauran.

Haka zalika, yace, kungiyar ‘yan gyada dake Tafawa Balewa a shirye take wajen ci gaba da baiwa gwamnati cikakken hadin kan da ya kamata domin kara bunkasa harkokin kasuwancin kayayyakin amfanin gona a fadin kasar nan.

Shugaban matasan kungiyar ‘yan gyada, Alh. Aminu Inuwa, ya shawarci ‘Yan kungiyarsa da su ci gaba da baiwa gwamnati da kungiyar cikakken goyan baya yadda ya kamata domin bunkasar tattalin arzikin jihar Kano da ma kasa baki daya.

 

 

 

Leave a Comment