Da Dumi-Dumi

Zamu Mayar Da Yaran Da Basa Zuwa Makaranta Komawa Karatu a Fadin Jihar Kano

Written by Pyramid FM Kano

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar Kano zata cigaba da hada hannu da kungiyar tarayyar turai wajen mayar da yaran da basa zuwa makaranta komawa karatu a fadin jihar.

mataimakin gwamnan jihar Kano kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne a madadin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba kabir yusuf ya furta hakan a wajen wani taro da aka shiryawa ayarin kungiyar tarayyar turai a matsayin cigaba da ziyarar da suka kawo jihar kano wanda ya gudana a dakin taro na Afficent dake Sultan Road a Kano.

Kwamared Abdussalam ya bayyana cewar akwai yara sama da miliyan daya da basa zuwa makaranta wanda daga cikinsu akwai maza da mata.

Ya kuma bayyana cewar a kokarin Gwamnatin su na farfado da ilimi sun tura kwararrun malamai sama da dubu shida makarantu daban daban domin koyarwa a jihar nan.

Ya kara da cewar Gwamnatinsu ta kuma tura dalibai dubu daya da dari daya jami’o’i dake kasashen ketare daban daban domin yin karatun digiri na biyu.

Anata bangaren shugabar ayarin kungiyar tarayyar turai Ambasada Samuela Tapiola ta bayyana cewar wannan taro da wannan ziyara itace irinta ta farko da kungiyar ta taba yi a nahiyar Africa kuma kungiyar ta zabi kano ne saboda muhimmancin da take baiwa ilimi tare kuma da yawan alumma da take dashi wanda mafi akasarin su matasa ne.

Ta kuma bayyana cewar wakilai goma sha takwas daga cikin jami’o’i 23 na kungiyar tarayyar turai sun halarci wannan taron da yake gudana kuma Sun zo ne domin hada hannu da gwamnati ta yadda zaa rika tura yara karo karatu kasashen ketare.

Wakilinmu ya ruwaito cewar daga cikin mahalarta taron akwai kwamishinoni, daraktoci, dalibai da kuma masu yiwa kasa hidima.

Leave a Comment