Labaran Duniya Labaran Jiha Muhalli

Zamu Kashe Miliyan 70 a Fadada Magudanan ruwan Shataletalen Baban Gwari — Kabiru Getso

Written by Pyramid FM Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta kashe Naira Miliyan 70 wajen sake fadada Magudanan ruwan da ta hade zuwa Shataletalen Baban Gwari a nan kwaryar birnin Kano.

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan bayan kammala tsafar Muhalli ta Asabar din karshen watan Afirilun 2022.

Ya ce aikin wanda hadin gwiwa ne tsakanin ma’aikatar Muhalli da hukumar rayawa da tsara birane ta jihar Kano KNUPDA an yi shi ne domin fadada Magudanan ruwan wacce take tara ruwa Mai tarin yawa musamman a lokutan damuna.

Dakta Kabiru Getso ya kuma bayyana takaicin sa kan yadda ake gudanar da harkokin kasuwanci a bakin kasuwar kusa filin wasa na Ado Bayero Square duk da kasancewar ta a rufe, ya na mai cewar kwamitin koli na tsafar Muhalli ya bada umarnin dabe dukkan teburan wanda suka karya dokar.

“A wancan zuwan da mukayi mun sami kasuwar a bude ana hada-hada, Amma a wannan karon da muka je mun same ta a rufe, Amma abin takaicin shine yadda wasu sun saka tebura a wajen kasuwar, da ma wanda suke kasuwanci akan titi, gaba daya Titin ma an rufe shi ana gudanar da kasuwanci a kai, kuma abin bakin cikin ma an zuzzubar da ruwa, mun ga mai markade ma, sun bata tatin wanda hakan ma zai kawo lalacewar titin da gwamnatin ta kashe makudan kudade wajen ginawa al’ummar yankin”, inji Getso.

Ku karanta: Kotu Ta Ki Amincewa A Mayar Da Shari’ar Abduljabbar Abuja

Ya ce “saboda haka wasu daga cikin su mai shara’a yayi musu tara a nan take, wasu kuma mun debo teburan su, mun ce musu su zo su samemi a ma’aikatar Muhalli, kuma hikimar yin hakan shine su zo mu tattauna da su da Shugabanni kasuwar da dukka masu ruwa da tsaki da nufin a samar da masalaha domin ganin hakan bai cigaba da faruwa ba”.

Ya cigaba da bukatar al’ummar da su guji zubar da shara a Magudanan ruwa la’akari da lokacin damuna da ake ciki, yana Mai cewa ko a karatowar damuna Gwamnatin jihar Kano ta a yashe mita dubu saba’in (70,000) na magudanan ruwa domin gujewa ambaliya.

Kididdiga ta nuna cewa a yayin tsaftar Muhalli kotun tafi da gidan ka ta tsaftar Muhalli ta kama mutane 69 da lefin karya doka inda aka yi musu tarar naira dubu saba’in da daya (71,000).

Leave a Comment