Kasuwanci

Zamu Kawo Karshen Shigo Da Gurbatattun Magunguna A Cikin Jihar Kano

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar masu sana’ar siyar da magunguna ta kasa reshen jihar Kano, ta jaddada ci gaba da kudirinta na kakkabe batagarin mutane da suke siyar da gurbatattun magunguna a fadin kasar nan.

Sakataren kungiyar ta jihar Kano, Alh. Salisu Tijjani Datti ne ya jaddada haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da nasarorin da kungiyar ta samu a ofishinsa dake nan jihar Kano.

Alh Salisu Tijjani Datti yace, kungiyar masu kasuwancin magunguna ta jihar Kano, ta samu nasarar dakile yawan kawo gurbatattun magunguna ta hanyar hadin gwuiwa da Hukumomin tsaro da suka hadar da; hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi da jami’an ‘yan sanda da Hukumar kula ingancin Abinci da magunguna ta kasa da Hukumar kula da hakkin mai siye da siyarwa ta jihar Kano da sauran jami’an tsaro.

Sakataren ya bayyana cewa, kungiyar tana mutukar farin ciki bisa hadin kan da hukumomin suke baiwa kungiyar na cika kudirinta da ta sanya akan gaba, domin kawo karshen yawan shigowa da magungunan da basu da inganci zuwa cikin birnin Kano da kewaye.

Sakataren yace, a wani bincike da kungiyar ta yi a kwanan nan ta gano cewa da yawa mutane da suke siyar da magunguna gurbatattu da na sanya maye ba ma sana’ar siyar da magunguna suke yi ba a jihar Kano da ma kasa baki daya.

Ya kara da cewa, wannan ta sanya kungiyar ta sake kafa wani kwamatin kar ta kwana da zai fara bibiyar irin wadannan masu laifi domin ganin ta kakkabesu daga shiga hurumin da ba nasu ba inda yace, yin haka zai rage yawan batawa ‘Yan kasuwar magunguna suna a fadin jihar Kano da ma kasa baki daya.

Haka zalika kungiyar ta yi kira ga gwamnati da al’ummar jihar nan da su baiwa yunkurin kungiyar hadin kan domin kare matasa da sauran jama’a shiga munanan hali a kasa baki daya.

Yace, hakan ba zai yiyu ba, dole sai al’umma sun baiwa kungiyar goyan baya ta hanyoyin da suka kamata, inda yace, yanzu an samu raguwar masu shigo da gurbatattun magunguna da na maye a jihar Kano, sakamakon damba da kungiyar ta dauka da hadin kan hukumomin tsaro na kasa da Kano baki daya.

Daga karshe ya shawarci masu shigo da gurbatattun magunguna da wadanda suke sanya maye, da su ajiye makamansu na wannan ta’ada domin duk wanda hukumomin suka kama da laifi ba su raga masa ba, domin harkace da bata kamata kuma, doka ce a kundin tsari kasar nan.

 

Leave a Comment