Labaran Jiha Uncategorized

Zamu Inganta Sha’anin Tsaro Ta Yadda Kowacce Jiha A Nijeriya Sai Tayi Koyi Damu

Written by Admin

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci wakilan kwamitin tsaro na majalisun tarayyar kasarnan su rubanya kokarin su wajen magance kalubalentsaro dake addabar kasarnan.

Mataimakin Gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo ne amadadin Gwamna Alhaji Abba kabir yusuf ya furta hakan lokacin da ya karbi bakuncin hadingwiwar kwamitin majalisun tarayyar kasarnan kan shaanin tsaro afadar gwamnatin jihar Kano.

Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya bukaci rundunar sojin kasarnan ta hada hannu da jihohi musammam wadanda ke makwabtaka da jihohin dake da matsalar tsaro domin kawo karshen sa a fadin kasarnan.

Kwamared ya kuma shawarci wakilan kwamitin su sadaukar dakai wajen gudanar da aikinsu, indaya basu tabbacin gwamnatin jihar kano wajen inganta shaanin tsaro a ciki da wajen jihar.

Shima anasa jawabin, shugaban kwamitin Alhaji Abdullahi Mamuda yace, sun zo Kano ne domin duba aikin yadda ake horas da kananan sojojin da aka dauka aiki wadanda ke sansanin horas da sojoji a dajin Falgore.

Daganan, sai ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa kokarin ta na inganta sha’anin tsaro kana kuma yayi godiya bisa irin karramawar da akayi musu.

Wakilinmu, ya ruwaito cewar, taron ya samu halarta wasu daraktoci da kuma wasu manyan jami’an gwamnati.

Leave a Comment