Kasuwanci

Zamu Inganta Kasuwar Singa Da Kewaye (SEMEDAN)

Written by Admin

Daga: Ibrahim Sani Gama

Shugabancin Kungiyar kasuwar Singa wato (SEMEDAN) ya jaddada kudirinsa na inganta lungu da sako na kasuwar domin cigar da al’ummar da kasuwar gaba.

Sakataren kungiyar Ibrahim Nafiu Abdullahi Mentos ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai Jim kadan bayan kaddamar da fara gyaran titinan dake fadin kasuwar.

Sakataren yace, kungiyar ‘Yan Kasuwar da hadin gwuiwar wasu dattijan kasuwar ne, suka hada hannu guri guda kasancewar an kwashe tsawon lokuta da tsuhuwar kungiyar ta Gaza yi, amma da zuwan wannan sabon shugabancin yayi ayyuka da dama a cikin Kasuwar Singa.

Ibrahim Nafiu Abdullahi yace, kungiyar ta Samar da motar kashe gobara Wanda yanzu kuma tana da aniyar aiwatar da ayyuka daban daban da za su inganta kasuwanci da taimakawa marasa karfi da suka hada da ‘Yan Dako da mayar da ‘ya’yan marasa karfi zuwa makarantu daban daban domin inganta rayuwarsu kamar kowa.

Sakataren kungiyar ya bayyana cewa, kamfanoni da dama da suke mu’amulla da ‘yan kasuwa a cikin wannan kasuwa da suka hadar da kamfanin Dangote da BUA da Aspira da kamfanin Mamuda da sauran manyan kamfanoni sun sha alwashin ba da tasu gagarumar gudunmawa wajen inganta lungu da sako na Kasuwar Singa yadda ya kamata.

Ibrahim Mentos ya kara da cewa, kungiyar ta yabawa wadan nan Kamfanoni da suke ba da wannan gudunmawa ta yau da kullum wajen tabbatar da kasuwanci ya samu gagarumar nasara a fadin jihar Kano da kasa baki daya.

Haka zalika Kungiyar kuma, yabawa dattawan wannan kasuwa da suka hadar da Alh. Salisu Sanbajo Alh. Adakawa da sauran ‘yan kasuwar da suke ba da gudunmawa wajen ganin kasuwanci jihar Kano da kasa ya ci gaba da rike kanbunsa yadda ya kamata,kasancewar jihar kano cibiya ce ta kasuwanci.

Kungiyar ta kuma ce, kofarta a bude take wajen bayar da shawarwari da gudunmawa wajen inganta lungu da sako na cikin Kasuwar Kwanar Singa dake nan birnin Kano.

Leave a Comment