Da Dumi-Dumi

Zamu Inganta Harkokin Masana’antu A Jihar Kano

Written by Admin

Daga; ADAMU DABO

Gwamnatin jihar Kano ta Yi kira ga masu hannu da shuni dama manya da kananan ‘yankasuwa dasu hada hannu da gwamnati wajen kawo cigaban jihar Kano.

Kiran ya fito ne daga bakin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yayin wata hira ta musamman da gwamnan yayi da kafafan yada labari a fadar gwamnatin jihar Kano.

Gwamna Yusuf ya ce ya zama wajibi gwamnati ta hada hannu da attajiran dake jihar Kano wajen Samar da harkokin inganta masana’antu a Jihar Kano.

Ya Kuma ce hakika masana’antu jihar Kano na bukatar kulawa ta musamman domin farfadowa.

Leave a Comment