Da Dumi-Dumi

Zamu Hada Hannu Da Kungiyar Tarayyar Turai Domin Bunkasa Ilimi A Jihar Kano

Written by Pyramid FM Kano

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na hada hannu da kungiyar tarayyar turai wajen bunkasa shaanin ilimi a fadin jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Kano kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne a madadin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya furta hakan a yayin da ayarin kungiyar tarayyar turai karkashin jagorancin Ambasada Samuela Tapiola suka kawo ziyarar ban girma a fadar Gwamnatin jihar.

Ya bayyana cewar akwai dadaddiyar alaka tsakanin kasarnan da kungiyar tarayyar turai.

Ya kuma yabawa kungiyar bisa wannan ziyara irinta ta farko da suka kawo jihar Kano.

Don haka ya bukacesu suyi amfani da wannan damar ta kawo ziyara wajen gano duk bangaren da zasu iya taimakawa.

Anata bangaren, shugabar ayarin kungiyar tarayyar turai din misis Samuela tace, sun ziyarci Kano ne saboda muhimmancin da take dashi a bangaren zamantakewa da tsarin mulki dana tattalin arziki.

Kuma sun zo ne a madadin iyalan kungiyar wadanda suka haura sama da ashirin a fadin kasashen turai.

Ta kuma bayyana cewar makasudin zuwansu jihar kano shine domin su bada tallafi a bangaren ilimi da harkar noma da da bangaren kimiyya da fasaha da sauran bangarori da zasu bunkasa tattalin arzikin jihar.

Daga cikin mahalarta taron, akwai kwamishinan ilimi dana ilimi mai zurfi da kwamishinan muhalli da sauran daraktoci na ma’aikatu daban daban.

Leave a Comment