Labaran Jiha

Zamu Hada Hannu Da Gwamnatin Jihar Kano Domin Habbaka Ayyukan More Rayuwa

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bukaci cibiyar gidauniyar Dangote da ta karasa wasu muhimmin gine-gine dake cikin asibitin murtala a birnin Kano.

Gwamna Yusuf ya bukaci hakan ne yayin da ya karbi bakuncin Alhaji Aliko Dangote shugaban cibiyar gidauniyar Dangote foundation a fadar gwamnatin Kano.

Gwamna Yusuf, ya kuma bukaci Alhaji Aliko Dangote da ya tallafawa jihar Kano a bangarori da dama Kamar bangaran lafiya, noma da harkar ababan more rayuwa ga alummar jihar Kano.

Tun da fari dai, a nasa jawabin, Alhaji Aliko Dangote ya ce ya kawowa gwamna Yusuf ziyare ne domin tayashi murnar samun nasarar da yayi a kotun koli.

Dangote ya ce, Kano garinsane ya zama wajibi cibiyarsa ta hada hannu da gwamnatin jihar Kano domin habbaka ayyukan more rayuwa ga al’ummar jihar Kano.

Leave a Comment