Kasuwanci

Zamu Goyi Bayan Duk Jam’iyar Da Zata Karbo Hakkin Yan Kungiyar Mu da Aka kashe — Mustapha Ali

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama

Shugabancin kungiyar masu fataucin Shanu da dabbobi ta Kasa ta bayyana cewa a shirye take wajen goyon bayan duk jamiyyar siysar da za ta tallafawa ‘ya’yan marayun da wandanda suka samu karyar arziki sakamakon cin mutuncinsu da aka yi a lokacin rikice_rikicen da ya afku da yan kungiyar a kudancin kasar nan, domin inganta rayuwarsu.

Shugaban kungiyar Alhaji Mustafa Ali ne ya tabbatar da haka a zantawarsa da manema labarai a nan jihar Kano dangane da watsi da rashin cika alkawarin da Gwamnatin tarayya ta dauka na biyan yan kungiyar Asarar da suka yi a lokuta daban_daban a sassan jihohin kudancin kasar nan.

Mustafa Ali ya bayyana cewa kungiyar ta zauna da kungiyar Dattawan Arewa da manyan jigajigan Gwamnatin tarayya tare da hakurtar da ‘ya’yan kungiyar wajen daukar mataki saboda cin zarafi da kisan gilla da Asarar dukiyoyin da ake yiwa yan Arewa da suke kai Shanu da dabbobi zuwa kudu, amma, har yanzu Bata sauya zani ba.

Shugaban yace irin rashin daukar mataki da Gwamnatin tarayya da na jihohin basa yi yana haifar da matsaloli da dama, musamman wajen Samar da rashin cikakken tsaro da kawo rashin jituwa tsakanin kabilun dake zaman lafiya da juna inda ya ce Kofar kungiyar a bude take wajen baiwa duk wadanda za su bawa ‘yan kungiyar kulawar da ta dace wajen ganin an kara tallafawa ‘ya’yan ta a koina suke a fadin kasar nan.

Ku karanta: Zamu Sauya Tsarin Koyar da Sana’o’i da NUC ta zo da shi Don Samarwa Matasa Aiki — Farfesa Kurawa

Haka kuma, ya kara da cewa ‘ya’yan kungiyar sun tafka mutukar asara da rasa rayukan wadansu wadan suke da bukatar a biyasu Diyya domin ci gaba da kula da iyalansu da yanuwansu.

Ya ce a wani rahoto da kungiyar ta fitar sakamakon yawan cin mutuncin su da ake a kudancin Najeriya ya nuna cewa sun yi Asarar dukiya sama da miliyan 4,000 ban da Asarar rayuka tun Daga farkon Gwamnati Mai ci har zuwa yanzu, kuma babu wani taimako da aka yi musu da nufin rage musu radadin abin da akayi musu.

Shugaban kungiyar yayi kira ga shugabannin Arewa da masu Ruwa da tsaki da mahukuntan Arewacin Najeriya da su kasancewa masu kishin yanuwansu musamman wajen ganin sun karbo musu hakkokinsu domin samun cikakken tsaro da zaman lafiya.

Ya ce rashin cikakken kulawa ga irin wadannan matsaloli na Daga cikin abubuwan da suke kawo koma baya ta fannin harkokin tsaro da kasuwancinsu da farfado da tattalin arziki.

Ya ce Dattawan Arewa suna da rawar takawa a irin wannan lokacin da za su, yiwa shugabannin da abin ya Shafa magana ta hanyar da ta dace, shi ya sa suka nemi zama da su tun a lokutan baya domin lalubo bakin zaren matsalolin da suke afkuwa don kaucewa gudun tashin fitina, Wanda yin rigima ba abin da zai haifar sai koma baya a cikin fadin kasar nan.

“A don haka kungiyar ta masu fataucin Shanun ta Kasa ta ce, tana da alumma da dama a sassan jihohin Najeriya daban daban, kuma duk Dantakarar da ya taimakawa yan kungiyar, ko kungiyoyi da masu hannu da marayu da shugabanni to tabbas za su bashi gudunmawar da ta kamata domin samun damar taimakawa marayu da sauran alummar da suka rasa jairinsu saboda rashin kyautawa da takwarorin alummar kudancin kasar nan suka yi wa yankasuwar dake kai Shanu da dabbobi da sauran kayayyakin masarufin amfanin Yau da kullum a matsayin huddar kasuwanci”.

Daga nan Shugaban kungiyar ya kara da cewa Gwamnatin tarayya ya kamata ta tuna lokacin da kungiyar ta zauna tare da Neman hadin kan kungiyar domin Dakatar da aniyarta na lafiya yajin aikin kai Shanu da dabbobi, zuwa kudu da yi mata alkawarin biyanta Diyya bisa Asarar da aka janyo mata, Amma har Yau ba’a kai ga ciki wannan alkawarin ba.

Ya kuma shawarci yankungiyar da su ci gaba da Bata cikakkiyar gudunmawa da hadin kai domin ci gaba da taimaka musu da kare duk hakkokinsu a koda yaushe musamman wajen Samar da tsaro da bunkasar tattalin arziki da Samar da ayyukan yi ga Matasa domin kaucewa yawan shan muggun kwayoyi da aikata barna.

Leave a Comment