Kasuwanci

Zamu Dawo Da Martabar Kasuwanci Da Inganta Rayuwar Al’umma Kasuwar Singa

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Dan takarar Shugabancin Kungiyar Kasuwar Singa kuma, Shugaban kungiyar Kwankwasiyya ta kasuwar Singa, Alh Mutari Mohammed Liti Kwasamgwami, ya jaddada kudirinsa na kawo managartan shirye-shirye da za su bunkasa harkokin kasuwanci da Al’ummar dake kasuwanci a cikin kasuwar ta Singa.

Muntari Mohammed kwasamgwami, ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai dangane da yadda al’ummar kasuwar suke ta kiraye-kirayen ya fito domin shugabantar kungiyar kasuwar Singa.

Yace, duba da kiraye-kirayen da al’ummar kasuwar ke yi masa ya sanya ya ga dacewar ya fito domin daukar wannan nauyi na kawo gyare-gyare da bunkasa harkokin kasuwanci da ci gaban matasa da farfado da tattalin arzikin kasuwanci a jihar Kano.

Shugaban kungiyar ya sha alwashin hada kai da Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf na samar da magudanan ruwa a Kasuwar ta Singa domin kaucewa ambaliyar ruwa da kuma, taimakawa ‘Yan Dako saboda wahalar da suke samun kansu a lokacin Damina.

Muntari Kwasamgwami ya kuma bayyana cewa, Shugabancinsa zai nemi hadin kan Dattawan Kasuwar Singa da sauran manyan ‘Yan Kasuwa da kamfanoni manya domin su zo su hada hannu da kungiyar kasuwar wajen ganin an inganta harkokin kasuwanci a kasuwar ta Singa.

Shugaban kungiyar kwankwasiyyar dake kasuwar Singa, ya bukaci hadin kan al’umma manya, yara da dattawan wannan kasuwa da sauran al’ummar dake kasuwanci a lungu da sako na kasuwar da su marawa wannan tafiya baya yadda ya kamata domin cimma nasarar da aka sanya a gaba.

Ya kuma bayyana cewa, Shugabancinsa zai taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin gwamnati mai ci da aniyar jagoran Kwankwasiyya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso na zama Shugaban kasa na gobe. Inda yace, a shirye al’ummar dake kasuwanci a Kasuwar suke su ci gaba da marawa Gwamnatin jihar Kano baya wajen ganin an inganta rayuwar al’umma da ciyar da kasuwanci gaba.

Leave a Comment