Da Dumi-Dumi

Zamu dakile masu siyar da magani marasa inganci a Kano – Kungiyar masu magunguna.

From: Ibrahim SANI Gama

Shugaban kungiyar kasuwar masu sana’ar siyar da magunguna ta kasa reshen Jihar Kano, ya sha alwashin kawo karshen siyar da magungunan da wa’adinsu ya kare da magungunan da suke sanya maye domin dakile sha da fataucin miyagun kwayoyi a fadin Jihar Kano.

Shugaban kungiyar kasuwar Mohammed Musbahu Yahaya ne ya jaddada hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake malam kato a Jihar Kano.

Yace, kungiyar ta bijiro da kwamati da yake bibiyar ‘yan kasuwa da suke shigo da magunguna marasa inganci da wadanda suke shigo da miyagun kwayoyi domin siyarwa al’umma Wanda hakan ba karamar matsala bace ga al’ummar jihar musamman matasa wadanda sune shugabannin gobe.

Yace, wannan shine kudirin farko da kungiyar ta sanya a gaba saboda gagarumar matsalar da take haifarwa a rayuwar al’umma.

Mohammed Musbahu ya bayyana cewa, baya da haka, Kungiyar za ta hada kai da gwamnatin jihar, domin samarwa ‘ya’yenta tallafin jari da za su bunkasa harkokin kasuwancinsu, musamman duba da kyakykyawar alakar da take tsakanin kungiyar kasuwar da gwamnati, kasancewar kungiyar ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa gwamnatin saboda da dannesu da tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta rinkayi.

Shugaban yace, kungiyar kasuwar a shirye take wajen baiwa Gwamnati cikakken goyan bayan da suka kamata domin inganta kasuwancin al’ummar jihar Kano.

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa bisa yadda wasu daga cikin ‘yan kasuwar suke neman sanya kananan ‘yan kasuwa su tashi zuwa kasuwar Dangwauro don ci gaba da kasuwaci acan, Inda ya bayyana cewa, Wanda gurin yayi matuar yiwa ‘yan kaswar tsada idan aka kwatanta da rukunin kasuwar da suke yanzu, wato, Karami Plaza.

Ya bayyana cewa, yanzu haka, ‘yan kasuwa suna biyan kudade kimanin Naira dubu Dari Uku (#300,000.00) a kowanne shago duk shekara, kuma, masu rukunin kasuwar sun samarwa al’umma jami’an tsaro da ruwa da wutar lantarki domin gudanar da kasuwacinsu yadda ya kamata.

Mohammed Yahaya yace, kasuwar Dangwauro tayi matukar yiwa ‘yan kasuwar tsada su biya har sama da Naira Miliyan Daya kudin haya a shekara, baya ga kuma, nisan da take da shi.

A don haka, wannan sabon shugabancin kungiyar kasuwar da ya zo, yake ta fafutukar samarwa ‘ya’yanta mafita akan kasuwancinsu, musamman uwar kungiyar kasuwar da ke babban birnin tarayya Abuja, Wanda yanzu haka, itace, ta dauki dawainiyar ragamar shari’ar da kungiyar kasuwar take yi akan komawa kasuwar ta Dangwauro dake Na’ibawa a nan Jihar Kano.

Uwar Kungiyar tace, wannan sabon shugabancin ya zo da managartan tsare-tsare da za su bunkasa harkokin kasuwancin al’ummar da kakkabe baragurbin mutane a harkar kasuwancin magani duba da dimbin al’ummar dake cin abinci da sana’ar musamman ma matasa wadanda yanzu sune suka fi yawa a kasuwancin.

Shugaban kungiyar kasuwar yace, sai dai babban abun da shugabancin kungiyar yake bukata bai wuce hadin kan ‘yan kungiyar ba, saboda sai da hadin kan ‘yan kungiyar ne, za ta samu damar bijiro da ayyuka da za su bunkasa harkokin kasuwancin jama’ar dake sana’ar a fadin Jihar Kano da ma kasa baki daya.

Haka zalika ya jaddada cewa, duk wani da zai kawo koma baya ko nakasu kungiyar kasuwar ba za ta gajiya ba wajen dakatar da shi daga yunkurinsa na lalata sana’ar, saboda zai yiyu wasu tsirarin mutane su dannewa wasu hakkokinsu ba.

Daga karshe ya bayyana gamsuwarsa bisa yadda Gwamnatin Jihar Kano take baiwa kungiyar goyan bayan da suka kamata domin sauke nauyin da Allah ya dora mata a matsayin uwar kowa a fadin jihar.

Leave a Comment