Muhalli

Zamu Cigaba da Bawa Gwamnati Hadin Kai Don Kwashe Sharar Kano — Kungiyar Direbobin Tifa

Written by Pyramid FM Kano

Kungiyar Direbobin Tifa ta jihar Kano ta ce zata ci gaba da aiki kafada-da-kafada da gwamnatin jihar Kano domin Kwashe sharar da ake tarawa a kwaryar birnin Kano da kewaye.

Shugaban kungiyar Ado Umar Santar-lungu ne ya bayyana hakan a lokacin tsaftar muhalli ta kasuwannin da maaikatu harma da hukumomin gwamnati a wani bangare na tsaftar Muhallin Watan Oktoban 2022 da muke ciki.

Shugaban ya bukaci ‘ya’yan kungiyar da su fito kamar yadda suka Saba a kowacce Asabar din karshen wata domin bada gudun mowar su don cigaban aikin tsaftar muhalli.

Ya ce kungiyar ta shafe tsawon shekaru tana gudanar da aiki kafada-da-kafada da gwamnati, kuma zata cigaba da aikin domin tabbatar da tsaftar muhalli.

Ku karanta: Za Mu Tattauna da Shugabannin Kasuwar Sharada Don Masalahar Tsaftar Muhalli — Kabiru Getso

“Muna kira ga duk ‘ya’yan wannan Kungiya da suka sami takardar gayyata da su ziyarci hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli REMASAB domin shan Mai tare da bin aikin kwashe sharar da aka tara a cikin kwaryar birnin Kano”, inji Santar-lungu.

Ado Santar-lungu ya kuma yabawa gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso bisa yadda suke tallafawa kungiyar tare da bata hadin Kai a duk lokacin da take gudanar da ayyukan ta.

Leave a Comment