Da Dumi-Dumi Ilimi

Zamu Ci Gaba Da Tallafawa ‘Ya’yan Wadanda Suka Rasu – Kungiyar Tsofaffin Daliban BUK

Written by Admin

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar Tsofafin Daliban Jami’ar Bayero ‘yan aji na shekarar dubu daya da dari tara da casa’in da tara, ta jaddada kudirin ta wajen tallafawa iyalan wadanda suka rasu dake cikin ungiyar domin inganta rayuwarsu yadda ya kamata.

Shugaban Kungiyar Alhaji Nura Ibrahim ne ya bayyana haka a lokacin gudanar da taron kungiyar na shekara shekara wanda ya gudana a helkwatar kula da harkokin yawan bude ido ta jihar Kano.

Shugaban yace, kungiyar na aiwatar da irin wannan taron ne, domin tunawa da wadanda suka rasu da tallafawa iyalansu da kuma, wadanda basu da karfi a cikin kungiyar.

Yace, kungiyar za ta ci gaba da gudanar da irin wannan taron don sanin halin da ‘ya’yayenta suke ciki da kuma, taimaka musu domin su ma su ji dadin gudanar da rayuwarsu kamar kowa.

Sakataren Kungiyar Aliyu Umar Aliyu, ya bayyana cewa, gudanar da irin wannan taron, zai kara hada kan al’umma da bunkasa zumunci tsakanin juna ta hanyar tattaunawa da kowa.

Aliyu Umar yace, kungiyar Dalibai ‘Yan Ajin Shekarar (1999) kansu a hade yake da juna a koda yaushe, inda yace, amma duk da haka za su ci gaba da gudanar da taron har tsawon rayuwarsu.

A jawabinsa Shugaban Gidan Rediyon Tarayya Pyramid, Malam Abba Bashir wanda daya ne daga cikin jigajigan wannan kungiya, ya shawarci kungiyar da ta samar da tsarin da za’a rika cirar kudin da mutum yake da halin bayarwa a matsayin tallafi ta Asusunsa na Banki koda karshen wata ne, maimakon shawarwarin da wasu daga cikin ‘yan kungiyar suka bayar na cewar, “kungiyar ta samar da wani kasuwanci da za’a rika juya kudin kungiyar domin tallafawa ‘Ya’yanta da iyalan wadanda suka rasu.

Abba Bashir yace, idan aka ce za’a fara irin wannan tsarin juya kudi to zai iya haifar da nakasu da koma baya a cikin kungiyar.

‘Ya’yan kungiyar da dama ne suka halarci taron tare da ba da shawarwari daban-daban domin ciyar da kungiyar ta tsofaffin Daliban daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Alhaji Aliyu Diso da Dan Galadiman Buhindu Bagudu Murtala Abubakar da Wazirin Danbatta Mustapha Shehu da kuma Mata da dama wanda ‘Yan kungiyar ne da dai sauransu.

 

Leave a Comment