Da Dumi-Dumi

ZAMAN LAFIYA: Mata Sun Gudanar Da Taron Addu’a A Kano

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO 

Mata daga kananan hukumomin 44 na jahar Kano sun gudanar da taron Addu ‘a na musamman domin samun zaman lafiya a fadin jahar Kano .

Taran addu’ar ya guda na ne a karkashin shugaban in shiyoyin mata masu rike da mukamai daban daban na kananan hukumomin 44 na jam ‘iyar NNPP .

Taron Addu’ar ya gudana ne a karamar hukumar birni karkashin jagorancin mata masu rike da madafan iko na jam ‘iyyar NNPP.

Inda da dama suke Addu’ar samun zaman lafiya musamman awannan yanayi da ake ciki na jiran sakamakon shari ‘ar da ake ciki ta gwamnan Kano.

Haka zalika sun bayyana cewar fatansu Allah yasa Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya samu nasara tare da tabbacin nuna goyon bayansu ga reshi.

Leave a Comment