Siyasa

Zaben 2023: Ku Zabi Shugabanni Na Gari Kamar Gawuna — Tanko Yakasai

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Shehu Sulaiman Sharfadi

Shugaban yakin Neman zaben Dan takarar Gwamnan Kano a zaben shekarar 2023 a jamiyyar APC Dakta Umar Tanko yakasai ya shawarci al’ummar jihar Kano da kasa baki daya, da su kasance masu zabar nagartattun mutane da za su kula da hakkokinsu da sauke nauyi da alkawarin da suka dauka a lokutan yakin Neman zabe.

Umar Tanko Yakasai ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da gwanayensa Dantakarar shugabancin kasa Asiwaju Bola Ahmed Tunubu da Dakta Nasiru Yusuf Gawuna bisa gudunmawar da suka bayar a lokutan da suka gabata, wanda ya gudana a gidansa dake nan Kano.

Yace Alummar jihar Kano, mutane ne da suke da ilimi da basira da ajiye abubuwan tarihi akan duk wasu shugabanni da suka jagarancesu inda ya ce alumma sun San Waye Gawuna da rawar daya taka tun daga shugabancin karamar hukumar Nassarawa da kwamishinan Gona har zuwa mataimakin Gwamnan, yana Mai cewa koda wannan ya kamata alumma su bibiya tare da dorashi a mizani domin zabarsa a matsayin Gwamnan Kano a 2023.

Ya ce dan takarar gwamnan ya tallafawa alumma ta fannoni da dama da suka hadar da baiwa dalibai tallafin karatu da Samar da magudanan ruwa da bunkasa kasuwanci musamman, bangaren harkokin Noma da taimakawa matasa da kungiyoyi da dama.

Yakasai ya kara da cewa, ta bangaren kyakyawar muamulla da jama,a bashi da fishin kowa ko gaba da wasu ko cin mutuncin abokanan burmin siyasa saboda basa tutar jamiyya guda, inda ya ce yana girmama manya da malamai da sauran alummar jihar Kano da kasa baki daya.

Ku karanta: Ku Guji Shiga Bangar Siyasa, Sakon Dan-jummai ga Matasan Kwasangwami

Ya sha alwashin cewa idan ya zama Gwamnan Kano a zaben shekara ta 2023, tabbas zai cikawa alummar jihar Kano alkawarirrikan da jamiyyar APC ta dauka tun daga kasa har jiha suka daukar musu da suka hadar da samar da tsaro da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Samar da tsaro yana daga cikin jigon ci gaban kowacce kasa, saboda idon babu tsaro babu kwanciyar hankalin jama’a sai kuma farfado da tattalin arziki wanda ya shafi fannoni da dama na rayuwar alumma.

Dakt Yakasai, ya ce akan haka Dan takarar shugabancin kasar nan a jamiyyar APC Bola Ahmed Tunubu ya samar da littafi mai dauke da manufofin da jamiyyar APC za ta fara kallo da zararar sun samu darewa kan shugabancin kasar nan a 2023.

Daga cikin abubuwan da suka fitar akwai farfado da kamfanonin da suka durkushe da samar da wutar lantarki da bunkasa kasuwanci da noma da samar da gidaje ga alummar kasa domin su samu saukin mallakar nasu da tallafawa fannin harkokin ilimi da Samar da sana’o’in dogaro da kai ga matasan yankunan kudu da arewacin kasar nan ta hanyar amfani da ilimin kimiyya da fasahar sadarwar zamani domin yakar talauci a jihohin kasar nan baki daya.

Ku Karanta: Zaben Kungiyar Yan Jaridu Na Pyramid: Za Mu Samar Da Kwamitin Da Zai Aiwatar da Manufofin Mu — Aminu Kwaru

Ya ce wannan ba zai samu ba sai alummar jihar kano sun ba da hadin kan daya dace wajen samarwa yan takaa jamiyyar APC tun daga jihohi har kasa baki daya.

Ya kuma shawarci alummar jihar kano da su kasance masu kulawa da sanya yan takara a mizani domin samar da shugabanni na gari da za su bunkasa kasa da alummarta ta bangarori da dama, yadda kasar nan za ta yi gogayya da sauran kasashen Duniya.

Ya kara da cewa, jamiyyar APC ta shirya tsaf wajen samarwa yankasa sauye sauyen da suka kamata, kasancewar alumma suna bukatar tallafin gaggawa da za su inganta rayuwarsu da alfahari da wanda suka jajirce wajen zabarsu inda ya ce ba za su baiwa maras ‘Da’ kunya ba.

Leave a Comment