Ilimi Siyasa

Ku Tsaftace Kalaman Ku Domin Gudun Cin Mutuncin Abokan Hamayya, Sakon Isa Nasidi Ga Yan Siyasa.

Written by Pyramid FM Kano

Shugaban Kamfanin “Noise Free Media Consult” Isa Nasidi ya bukaci ‘Yan Siyasa a Nigeria da su guji yin Kalaman batanci ga abokan hamayya ko su rika kalaman da zasu iya tunzira mutane aikata lefuka da ka iya janyo karancin zaman lafiya kafin da lokacin da kuma bayan zabe.

Isa Nasidi wanda kuma dalibi ne a digiri na Uku (Phd) a jam’iar Gwamnatin Tarayya dake Nsukka ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da manema labarai dangane da wasu litattafai da ya rubuta da suka mayar da hankali akan kalaman ‘Yan Siyasa da Masu magana a gidajen Radio (Sojojin baka kamar yadda ake Kiran su a Kano) da kuma kalamai a kafafen sada zumunta na zamani (Soshiyal Midiya) wanda ya gudana a nan Kano.

Ya ce a binciken da ya gudanar a hukuncin da Katuna daban-daban suka Yanke a nan Kano ya gano cewa sau da yawa ana samun sojojin bakar da lefin yin Kage da muzanta abokan hamayyar su ta siyasa, yana mai cewa a Mafi yana lokuta ana amfani da sojojin bakan ne wajen cimma muradan siyasa domin su kare ko su zuga ko su kushe wani sakamakon Zalakar zance da suke da shi.

Ku Karanta: Mun Shirya Ceto Kano, Inganta Kasuwanci Da Gina Al’umma Idan Mukayi Nasarar Cin Zabe — Tanko Yakasai

“Zarge-zargen da ake musu a Mafi yawan lokaci gaskiya ne domin na bibiyi wasu hukunce-hukuncen kotuna a nan Kano inda na gano cewa an kamasu da laifin yada karairayi da cin zarafin mutane da Kage”, inji shi.

A cewarsa “Sannan da na ziyarci hukumar NBC (Hukumar kula da gidajen Radio da Talabijin) na gano cewa wadannan ‘yan bakar sun sha jawowa gidajen Radio Tara ko Horo”.

Isa Nasidi ya ce Yan jarida suna da rawar da zasu taka na tabbatar da ta ce dukkan abubuwan da mutane yakamata su saurara a radio tare da taka burki ga Yan Siyasa masu kalaman da zasu iya bata sunan wasu, duk da cewa a wasu lokutan manyan Yan Siyasa ne ke matsa musu domin ganin sun yi abin da ya saba kaida.

Ku Karanta: Zaben Kungiyar Yan Jaridu Na Pyramid: Za Mu Samar Da Kwamitin Da Zai Aiwatar da Manufofin Mu — Aminu Kwaru

Haka Kuma, Isa ya ce a littafin da ya rubuta yayi bayanin menene labarai karya (Fake News) da yadda ake gane shi da kuma ilolinsa ga al’umma, yana mai cewa an bugashi da turanci da kuma Hausa ta yadda al’umma zasu iya saurara Musamman ga wandanda basu iya karatu da rubutu ba ko ga masu bincike.

Marubucin wanda kuma Dan jarida ne ya shawarci Yan jaridu a Kano dama Nigeria da su tabbatar da tantance gami da tace abubuwan da zai je kunnen jama’a la’akari da irin gudun mowa da tasirin su a tsakanin al’umma.

Ya kuma bada sharwarin da yakamata gwamnatoci da hukumomin da maaikatu da ma dukka masu ruwa da tsaki zasu bi domin dakile matsalar.

Daga bisani ya ce kofarsa a Bude take ga hukumomi da ma’aikatu ko dai-dai kun mutane domin hada kai wajen siyan kwafin littafin tare da rabashi ga al’umma domin amfanarsu.

Ga Mai son tattaunawa ko Bada gudun mowa za’a iya samun Isa Nasidi a isanyaya@gmail.com ko 08091753170

Leave a Comment