Kasuwanci

Zabe Ba Gudu Ba Ja Da Baya

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar kasuwar Singa karkashin kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa ta (AMATA) ta jaddada kudirinta na gudanar da zabenta yadda ya kamata.

Shugaban kungiyar na kasa kuma, shugaban kwamatin shirya Zaben kasuwar ta Singa Alh. Umaru Hussaini Gabaru Kiru ne, ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa manema labarai karin haske dangane da zaben Kungiyar kasuwar dake tafe.

Alh. Umaru Hussaini Gabaru yace, kwamatin gudanar da zaben kungiyar kasuwar ba zai Dakatar da duk wasu shirye-shiryensa daya sanya a gaba ba, inda yace, duk tsare tsare sun yi nisa na tabbatar da an gudanar da zaben kungiyar cikin hankali da lumana batare da wata tangarda ba.

A don haka, yake kira ga ‘yan takara da su zama cikin shirin da ya dace domin gabatar da zaben kungiyar kasuwar ta Singa cikin wasu ‘yan lokuta masu zuwa inda ya bayyana cewa, idan ban da an dan sami wani tsaiko da tuni an gudanar da zaben kungiyar.

Haka zalika, Shugaban ya shawarci kananan kungiyoyin dake cikin kasuwar mSinga, da su a hada kai guri guda domin ganin an ciyar da kasuwar a ‘yan kasuwarta gaba.

Yace, wadanda suke ta korafe korafe na kungiyoyin ne da suke kokarin sai sun haifar da matsala tsakanin al’ummar kasuwa wanda yin hakan ba daidai bane, kamar wata hanya ce ta rarraba kawunan al’ummar kasuwa da kasuwanci.

 

Leave a Comment