Yanzu-Yanzu

Zabar Abba Kabir Alkairi ne ga jihar kano – Barrister Dederi

 

By: Mukhtar Yahaya Shehu.

Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Karaye da Rogo Barrister Haruna Dederi ya bayyana zabar Abba Kabir Yusuf na jami’yyar NNPP a matsayin gwamna da cewa alkairi ne ga jihar kano.

Cikin sakon taya murnar lashe zaben gwamna mai dauke da sa hannun Sulaiman Dederi, dan majalisar na tarayya ya bayyana cewa Abba Kabir Yusuf yana da jajirce wa a sha’anin shugabanci a duk mukaman da ya rike a baya.

Barrister Haruna Dederi ya yi fatan samun nasara a sha’anin mulkin jihar kano da Allah Ya bashi bayan kammala zaben gwamna da na ‘yan majalisun dokoki da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata.

Ya Kuma taya sauran dukkanin wadanda suka lashe zaben majalisun tarayya da na jiha karkashin jami’yyar NNPP murnar lashe zabukan.

Barrister Haruna Dederi ya Kuma yaba wa al’umar jihar kano bisa yadda suka gudanar da zabukan na ranekun 25 ga watan fabrairu da Kuma na ranar 25 ga wannan wata na Maris da muke ciki.

Leave a Comment