Ilimi

Za Mu Yi Amfani Da Duk Abin Da Ke Hannun Mu Domin Cigaban Kwalejin CAS — Ali Saadu Birnin-kudu

Written by Pyramid FM Kano

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Ali Sa’adu Birnin-kudu ya ce za su yi amfani da duk abin da ke Hannun su domin cigaban Kwalejin share fagen shiga jami’o’i ta kwaryar Birnin Kano da nufin cigaban Ilimi.

Ali Sa’adu Birnin-kudu ya bayyana hakan ne a taron kungiyar tsofaffin daliban Kwalejin da suka kammala a shekarar 1980 wanda ya gudana a harabar Kwalejin da ke kan titin zuwa filin jirgin Sama na nan Kano.

Tsohon gwamnan ya ce la’akari da irin gudun mowar da Kwalejin da ta bayar a rayuwar su, nauyi ne da ya rataya a wuyan su na daukar matakan da suka da ce domin cigaban ta.

Ya ce zasu tabbatar da daukar matakai daban-daban ciki harda yin aiki kafada-da-kafada da sauran masu ruwa da tsakin da hukumomi da gwamnatoci da ma sauran tsofaffin daliban Kwalejin da nufin hada Hanu domin cigaban ta.

“…. A dumbun mutanen da suka kammala wannan makaranta, da shekarun da aka dauka ana yaye dalibai a Kwalejin nan kuma a ce ni ake so inzo na shugabanci wannan taro, to wannan ya sa na sake kaskantar da kaina ga Allah, cike da godiya Gareshi saboda wannan karramawa da akayi min”, inji Birnin-kudu.

Ku Karanta: Zamu Sauya Tsarin Koyar da Sana’o’i da NUC ta zo da shi Don Samarwa Matasa Aiki — Farfesa Kurawa

Ya ce “bana mantawa masallaci da ake sallah a nan CAS akayi tunanin za’a mayar da shi na Juma’a, kuma ake so na jagoranci wannan hidima don a tabbatar wannan masallaci ya koma na Juma’a, a wannan lokaci da nazo na basu labarin yadda mukayi rayuwar a CAS”.

“Domin ni wallahi idan aka ce na lalubo wadansu da mukayi CAS da su ban san inda suke ba, amma ku gashi yanzu Kun dabbaka abun duk da shekaru 42 da kammala makarantar nan da kukayi, kuna da lambobin Juna, kuna ma’amala da juna, kuna zaunawa tare, wannan ba karamin abu bane”, inji Birnin-kudu.

A nasa bangaren, daya daga cikin malaman ‘yan kungiyar Dakta Faruk Umar ya bayyana farin cikin sa ganin daliban da ya koyar shekaru 42 da suka gabata sun girma tare da zama wasu ciki harda wanda ya rike mukamin Gwamnan jihar Jigawa.

Dakta Faruk Umar daga nan ya shawarci ‘yan ajin na shekarar 1980 da su kafa wata babbar kungiya da zata hada kan dukkan tsofaffin daliban makarantar tunda aka kafata.

“Kasancewar wannan taron shine na farko na kungiyar tsofaffin daliban wannan makaranta, akwai bukatar a hada kungiyar ta kasa da zata kunshi dukkan tsofaffin daliban wannan makaranta”, inji Dakta Faruk.

Tuni dai kafin tashi daga taron aka amince kwamitin da ya shirya taron ya jagoranci hada kan dukkan tsofaffin daliban makarantar tunda aka kafata da nufin kawo cigaba mai ma’ana.

Ku Karanta: Ku Kyauta Rayuwar Al’umma Da Kudaden Shigar Ku, Aminu Ado Ga Gwamnatoci

A jawabansu daban-daban, wadanda suka shirya taron Yusuf Abdallah da Kuma Hajiya Sa’a Ibrahim (Shugabar Gidan Talabijin ta Abubakar Rimi da ke nan Kano ARTV) sun ce sun shirya taron ne domin hada kan ‘yan uwansu da suka kammala karatu shekaru 42 da suka gabata da nufin sada zumunta a tsakanin su.

Sun ce yin hakan zai basu dama wajen cigaba da sada zumunci da tallafawa juna da hada kan iyalan su baki daya, inda suka sha alwashin cigaba da wanzar da zumuncin dake tsakanin su.

Sa’a Ibrahim a madadin ‘ya’yan kwamitin ta bada tabbacin yin aiki tukuru domin hada kan ‘ya’yan kungiyar a ko ina suke a fadin Duniya.

Da yake bayyana farin cikin sa, shugaban makarantar kuma mai neman zama Farfesa Sanusi Yakubu Ahmad ya ce abin alfaharin sa ne ganin yadda tsofaffin daliban makarantar da suka kammala tun yana karamin suka hada kansu domin tallafa mata.

Ya ce kasancewar wannan shine karon farko da ake shirya taron kungiyar tsofaffin daliban makarantar, abu ne Mai matukar fa’ida kuma zasu bada dukkan gudun mowar da ake bukata domin samun nasara.

Sanusi Yakubu Ahmad daga nan ya yabawa gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam bisa bada gudun mowa domin cigaban makarantar ciki harda wasu malamai kusan 120 da aka sauyawa gurin aiki daga wasu gurare zuwa Kwalejin.

Leave a Comment