Kasuwanci

Za Mu Yi Aiki Da Sale Kausani Don Bunkasa Harkokin Sufuri — Matuka Motocin Haya

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar matuka motocin haya ta kasa reshen tashar mota ta Malam Kato ta sha alwashin gudanar da ayyuka kafada da kafada da Sabon kwamishinan sufuri da gidaje na jihar Kano Alhaji Sale Kausani domin bunkasa harkokin sufuri a fadin jihar.

Shugaban matasan kungiyar Alhaji Samaila Gredy ne ya bayyana haka a lokacin da yake Karin haske ga manema labarai dangane da Sabon kwamishinan sufuri da gidaje da Gwamnatin jihar Kano ta nada, wanda ya gudana a ofishinsa dake tashar.

Shugaban ya ce kungiyar ta shirya tsaf domin neman damar tattaunawa da kwamishinan kasancewar akwai kudirce-kudirce da za su inganta harkokin sufuri dama zayyana masa matsalolin da gamayyar kungiyoyin sufuri suke fuskanta a wannan lokaci da muke ciki, inda ya ce, direbobi suna fuskantar kalubale ta Fannin sana’ar su daga bangarori da dama.

Ya ce, daga cikin kalubale da direbobi suke Fama da su, akwai rashin cikakken tsaro da rashin kyawawan hanyoyin da za su rika aiwatar da ayyukansu da cin zarafin direbobi da wasu daga cikin jamian tsaron hanya suke yiwa ‘ya’yan kungiyar.

Ku karanta: Zamu Goyi Bayan Duk Jam’iyar Da Zata Karbo Hakkin Yan Kungiyar Mu da Aka kashe — Mustapha Ali

Samaila Gredy, ya shawarci kwamishinan sufuri da gidaje Alhaji Sale Kausani, da ya amfani da wannan lokaci da yake ziyarce ziyarcen guraren dake karkashin Ma’aikatar sa domin ganin yadda alamura suke gudana, inda yayi kira da ya rika ziyartar tashoshin motocin haya domin sanin abubuwan da suke faruwa da kuma, ganewa idanunsa yadda alamura suke tafiya.

Shugaban matasan ya ce, rashin tattaunawa da kungiyoyin su na direbobi ya na daya daga cikin abubuwan da suke kawo koma baya da durkushewa harkokin sufuri, saboda direbobi ne za su bayyana Maka halin da suke tsintar kansu a ciki, sabanin tuntubar wadanda ba Sana’ar su bace.

Haka zalika, ya ce kungiyar tana ragewa Gwamnati nauye nauye ta fannoni da dama, musamman ta hanyar samarwa matasa ayyukan yi da samar da kudaden haraji wanda sune ake gudanar da ayyuka na musamman da na raya karkara da sauran harkokin ci gaba.

Daga nan yayi kira ga yan kungiyar da su kara baiwa Kungiyar cikakken hadin Kan daya dace domin ciyar da kungiyar gaba.

Leave a Comment