Kasuwanci Muhalli

Za Mu Tattauna da Shugabannin Kasuwar Sharada Don Masalahar Tsaftar Muhalli — Kabiru Getso

Written by Pyramid FM Kano

Ma’aikatar Muhalli ta jihar Kano ta ce zata tattauna da Shugabannin Kasuwar Sharada dake yankin karamar hukumar birni da Kewaye domin lalubo hanyoyin da za’a magance matsalar tsaftar Muhalli a Kasuwar.

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan bayan kammala tsaftar Muhalli ta Kasuwanni da ma’aikatu Harma da hukumomin gwamnati da ake gudanarwa a duk Juma’ar karshen wata a nan Kano.

Dakata Kabiru Getso ya ce sun gamsu da yadda ake gudanar da tsaftar Muhalli a cikin Kasuwar, amma akwai bukatar a tattauna da su domin samar da Masalaha dangane guraren da ake siyar da Kayan Miya da kuma inda ake sayar da rake.

Kwamishinan ya ce ma’aikatar a shirye ta ke ta yi aiki da dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da tsaftar guraren sana’o’i da Kasuwanni da nufin kula da lafiyar al’umma.

Ku karanta: Tsaftar Muhalli: An ci Tarar Tashar Motar Rijiyar Zaki Dubu 100, Kowacce Mota Dubu 10

Daga nan ya yabawa Kamfanin filawa Mill da Kamfanin da suke sarrafa buhun bakko bisa yadda suke kula da tsaftar Muhalli, musamman yadda ake amfani da kayayyakin kariya a Kamfanin Bakko dake Sharada a cikin kwaryar birnin Kano.

A jawabinsa, shugaban Kasuwar Malam Hudu Abdullahi ya bayyana farin cikin sa dangane da ziyarar da ya ce zata karfafa musu gwiwar gudanar da ayyukan tsaftar Muhalli a Kasuwar.

Hudu Abdullahi daga nan ya Bada tabbacin aiwatar da dukkan gyare-gyaren da ka’idojin da aka basu domin kula da lafiyar al’umma.

Leave a Comment