Yanzu-Yanzu

Za mu tallafawa gwamna Abba Kabir da dokokin ciyar da Kano gaba – Hafizu Sharif

By: Mukhtar Yahaya Shehu

Zababben Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Bunkure Hafizu Sharif Gambo ya yi alwashin ganin sun tallafawa gwamna Abba Kabir Yusuf wajen samar da dokokin da za su ciyar da jihar Kano gaba.

Hafizu Sharif Gambo ya bayyana haka a sakonsa na fatan alkairi ga sabon zababben gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da jagoran jami’yyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Kuma al’ummar karamar hukumar Bunkure.

Ya ce a matsayin su na zababbun ‘yan majalisar dokokin jihar Kano za su yi duk me yi wu wa domin hada hannu da bangaren gwamnati domin ciyar da jihar Kanon gaba.

Dan majalisar Hafizu Sharif Gambo ya Kuma yaba wa al’umar jihar Kano bisa yadda suka gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da na gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jiha cikin kwanciyar hankali.

Ya Kuma yaba wa al’umar karamar hukumar Bukure bisa yadda suka kada wa jami’yyar NNPP kuri’un su, inda ya yi alwashin ganin sun bai wa mara Da kunya wajen wakilci na gari.

Leave a Comment