Siyasa

Za Mu Mayar da Hankalin Bunkasa Fannoni Shida Don Gina Sabuwar Kano — Tanko Yakasai

Written by Pyramid FM Kano

Jam’iyar PRP mai Alamar Dan Mukulli ta sha Alwashin mayar da hankali a Bunkasa fannoni shida (6) domin Gina sabuwar Kano matukar ta yi nasara a zaben 2023 da ke tafe.

Dan takarar gwamnan na jam’iyar Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana hakan bayan kammala kaddamar da manufofin da kuma shafin jam’iyar na internet wato www.dawisu.com da abubuwan da zai sa a gaba matukar yayi nasara a 2023.

Ya ce zasu mayar da hankali akan Tabbatar da tsaro da Bunkasa fannin ilimi da cigaban tsaftar Muhalli da Samar da ababen more rayuwa da Bunkasa fannin sifuri da kuma uwa-uba Bunkasa tattalin arziki jihar.

Ya ce zai tabbatar jihar Kano ta na samun kudin shiga na Dala miliyan 25 maimakon Dala miliyan 12 da jihar Kano take samu a yanzu.

Yayi fatan al’ummar jihar Kano zasu basu dama domin gina sabuwar Kano da kuma karbe ta daga hanun wadanda ya Kira ‘yan Wuru-wuru da hauma-hauma.

“Za mu tabbatar da farfado da darajar jihar Kano, kowa ya san yadda Kano take da daraja a lokacin mulkin tsohon gwamna Alhaji Audu Bako da Muhammadu Abubakar Rimi karkashin wannan jam’iya ta mu ta PRP, a wannan lokaci kowa yaga irin nasarar da aka samu, talaka bai taba sharbar romon dumukuradiyya ba kamar wannan lokaci, komai ya na tafiya a tsari da inganci, Amma Allah da ikon tun daga karshen mulkin PRP Abubawa suka Rika tabarbarewa har ya zuwa lokacin da muka samu kamu a ciki a yanzu”, inji Tanko Yakasai.

Ku karanta: 2023: Za Tabbatar An Zabi Shugabanni na Gari — Gidauniyar Ibrahim Khalil

“A shekarau dubu (1,000) kowa ya san jihar Kano a harkar kasuwanci, indan ka dauki jihar Kano ta Kai Matsayin wata kasa a Africa, Kusan yanzu ana maganar mutane miliyan ashirin ne a Kano kawai, a bangaren tattalin arziki ma tana da matukar karfi a Nigeria da Africa ma Baki daya, Kusan yanzu idan kana maganar kasashen da suka ci gaba a Africa zaka saka Rwanda, Amma jihar Kano ta fita yawan mutane da wasu abubuwan cigaba”, inji Yakasai.

A jawabinsa, dan takarar a jam’iyar ta PRP a jihar Kaduna Hayatuddeen Lawan Makarfi ya ce abin farin ciki ne kan yadda jam’iyar ta kaddamar da manufofin ta ga alummar jihar Kano domin babu wata jam’iya da tayi hakan a nan Kano.

Ya ce suma zasu gabatarwa alummar jihar Kaduna nasu manufofin wanda idan sukayi nasara zasu fi mayar da hankali akan su.

A wani cigaban labarin kuma, Dan takarar gwamna a jihar Jigawa a jam’iyar ta PRP Group Captain Ahmad Adamu Kaugama ya sha Alwashin daukar matakan da baza a sake samun ambaliyar ruwa a jihar ba.

Ahmad Adamu Kaugama ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da ‘yan jaridu Jim kadan bayan takawaransa na Nan Kano ya kammala gabatar da manufofinsa da zai aiwatar matukar yayi nasara a zaben 2023 da ke tafe.

Ku karanta: Ina Neman Afuwar Duk Wanda Na Batawa — Hafizu Kawu

Ya ce nuna halin ko in kula daga wajen gwamnatocin da suka gabata ya matukar bada gudun mowar samun ambaliyar ruwan da jihar ta fuskanta a damunar bana wacce tayi sanadin asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce matukar yayi nasara a zaben 2023 da ke tafe zai mayar da hankali wajen aiwatar da tsare-tsaren da zasu tabbatar da cigaban harkokin Noma da tabbatar da jihar bata sake fuskantar ambaliyar ruwa da ta yashe gonakin mutane ba.

Yayi fatan al’umma zasu basu dama domin ciyar da jihar ta Jigawa gaba.

Leave a Comment