Labaran Jiha

Za Mu Kawo Karshen Matsalar Ruwa A Karamar Hukumar Kura – Yahaya Kura

Written by Admin

Daga: MUKHTAR YAHAYA SHEHU

Jami’in rikon karamar hukumar Kura Alh Yahaya Tijjani Kura ya sha alwashin kawo karshen matsalar ruwan sha da ta dade tana addabar yankin.

Alh Yahaya Tijjani Kura ya bayyana haka ne yayin da ya jagoranci Kwamitin Ruwan sha na yankin karkashin Alh Aminu da ziyarar gaggawa dan ganin jalin da cibiyoyin samar da ruwan sha na Karamar Hukumar ke ciki.

Alhaji Yahaya Tijjani Kura ya bayyana rashin jin dadinsa bisa ganin yadda cibiyoyin samar da ruwan ba sa aiki kamar yadda ya kamata.

Jami’in rikon Alh Yahaya Tijjani Kura nan take ya bayar da umarnin gyaran matatar ruwa ta garin Karfi domin sanarwa da al’ummar yankin tsaftatancen ruwan sha.

Shugaban ya kuma nuna takaicin sa bisa yadda al’ummar garin Karfi suka shafe shekaru tara ba tare da samun ruwan Fanfo ba.

Shugaban Karamar Hukumar
Alh Yahaya Tijjani Alhaji Yahaya Tijjani Kura ya kuma bayyana takaicin sa bisa yadda ya ga halin da Kasuwar Karamar Hukumar Kura ke ciki ta fuskar tara kudaden shiga.

Shima shuaban kwamitin ruwan na Karamar Hukumar ta Kura, Alh Aminu Sharif yayi karin haske kan ziyarar da suka kaiwa shugaban karamar hukumar Alh Yahaya Tijjani da kuma yadda ya jagoranci kwamitin ziyarar gani da ido cibiyoyin samar da ruwan sha na Karamar Hukumar.

Leave a Comment