Labaran Jiha Muhalli

Mun Dasa Bishiyoyi Miliyan Hudu Cikin Shekaru Uku – Kabiru Getso

Written by Pyramid FM Kano

A kokarinta na magance kalubalen muhalli musamman zaizayar kasa da kwararowar hamada da dumamar yanayi, gwamnatin jihar Kano ta ce ta dasa bishiyoyi miliyan hudu cikin shekaru uku.

Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da dashen bishiyoyi na shekarar 2022 zango na farko da aka gudanar a unguwar Dakata dake yankin karamar hukumar Nasarawa ta nan Kano.

Ya ce a shekarar 2020 da aka dawo da aikin dasa bishiyoyi, an dasa guda miliyan biyu, a shekarar 2021 miliyan daya yayin da na bana gwamnatin jihar za ta dasa wasu bishiyoyi miliyan daya da nufin inganta Muhalli.

Dakta Getso ya ce “mai girma Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya dawo da dashen bishiyoyi, idan zaku iya tunawa a shekarun baya ana gudanar da aikin a duk shekara amma sai ya zama an dena, amma mai girma gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam ya farfado da aikin. Za ku iya tunawa a shekarar 2020 gwamnatin jihar Kano ta hannun ma’aikatar muhalli ta dasa bishiyoyi miliyan biyu, a shekarar da ta gabata 2021 mun dasa bishiyoyi miliyan daya, kashi na farko mai girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya kaddamar da shi a jami’ar Yusuf Maitama Sule, yayin da ni Kuma na kaddamar da kashi na biyu a unguwar Gama dake karamar hukumar Nasarawa”.

A cewar Getso shirin ya fi mayar da hankali kan yaki da matsalolin muhalli a jihar nan da suka hada da sauyin yanayi da kwararowar hamada da ambaliya ruwa da zaizayar kasa da kuma inganta Muhalli”. “Ya kara da cewa sauyin yanayi ya zama daya daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankali a duniya, shi ya sa gwamnatin jihar Kano ba a baya take ba wajen magance matsalar.

Ku karanta: Zamu Kashe Miliyan 70 a Fadada Magudanan ruwan Shataletalen Baban Gwari — Kabiru Getso

Ya ce a yankin Dakata kawai ma’aikatar za ta dasa bishiyoyi sama da dari hudu yayin da sauran al’ummomi da makarantu da coci-coci da masallatai da tituna da kungiyoyi za su ci gajiyar shirin.

“A ‘yan kwanakin nan muna fama da zafi sosai a nan Kano wanda baa saba yi ba, don haka wannan ya faru ne sakamakon sauyin yanayi, kuma daya daga cikin hanyoyin da za a magance sauyin yanayi cikin sauki shi ne ta hanyar dasa bishiyoyi don inganta Muhalli”, in ji kwamishinan.

Dakta Kabiru Getso ya ce a bana gwamnatin jihar za ta hada hannu da shugabannin al’umma da kungiyoyi wajen dasa bishiyoyi miliyan daya ta yadda za a kara samar da iskar iskar oxygen ga jama’a wanda zai rage gurbacewar iska a jihar Kano.

Ya ce, ma’aikatar za ta raba bishiyoyi ga makabartu, Masallatai, Makarantu da kungiyoyi daban-daban da nufin rage zafi a lokacin rani a jihar.

Kwamishinan ya yi kira ga jama’a da su guji sare bishiyoyi ba bisa ka’idaba kuma su guji zubar da shara a Magudanan ruwa yana mai cewa hakan zai kwao toshewar magudanan ruwa da ambaliyar ruwa da ka iya janyo asarar rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano.

Ku karanta: Dalilin da ya sa Gwamna Ganduje bai Zartar da hukuncin kisa ba ga wadanda suka kashe Hanifa

A nasa jawabin, Dagacin Dakata a karamar hukumar Nasarawa Alhaji Umar Faruk ya yaba jajircewar gwamnatin jihar sannan ya ce zasu tabbatar da kula da su.

Daga nan sai ya bukaci al’umma su yi koyi da ma’aikatar yana mai cewa ta hanyar yin haka Allah Ya saka musu da alheri sai nan zai inganta Muhalli da kula da lafiyar al’umma.

Leave a Comment