Lafiya

Za Mu Cigaba Da Bada Gagarumar Gudun Mowa a Bangaren Lafiya — Aminu Ado

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Muktar Yahaya Shehu

Masarautar Kano ta ce zata cigaba da bayar da Gagarumar Gudun Mowa wajen cigaban harkokin lafiya a jihar Kano da ma Arewacin Nigeria Baki daya.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ne ya bayyana hakan a wajen taron makon lafiya na shekara ta 2022 da Ma’aikatar lafiya ke shiryawa duk shekara kuma aka gudanar a dakin taro na Coronation dake gidan Gwamnatin jihar Kano.

Aminu Ado ya ce Masarautar ta Kano tana wayar dakan al’umma domin karbar aikace aikacen kiwon lafiya musamman rigakafin yau da kullum da rigakafin cutar Covid-19 da yaki da cutar shan-Inna Inda ya ce hakan yasa jihar Kano da kasa baki daya aka sami shaidar kawar da cutar a nan Kano.

Cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya ce masarautar ta nuna farin cikinsa bisa gudanar da taron tare da nasarorin da Gwamnatin Kano ta samu a bangaren lafiya karkashin Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje.

Ku karanta: Rejista Da Karbar Katin Dan Kasa Na Da Matukar Muhimmanci — Aminu Ado

Ado Bayero yayi bayanin cewa Gwamnatin jihar Kano tayi matukar kokari musamman idan akayi la’akari da yanayin da ake ciki na matsin tattalin arziki a duniya baki daya.

Ya taya Gwamnan kano murnar samun nasarori a fannin lafiya.

Mai Martaba Sarkin yayi fatan taron zai zama wani dandali na kara zage damtse domin cigaba da muhimman ayyuka da kuma zaburar da ma’aikata da al’umma wajen tallafawa shirye-shiryen kiwon lafiya.

Leave a Comment