Yanzu-Yanzu

Yunkurin Matasa kan ginin Kamfanin Jaridar Triumph.

By: MAGAJI ZAREWA

Sabbin rahotanni na faman yawo da Yammacin yau Lahadi daga karamar hukumar Fagge da ke Jihar Kano ta Arewa maso Yammacin Kasarnan na nuni kan cewar gangamin matasa sun kewaye tsohon gidan babban Kamfanin Jaridar Triumph dake damfare da sabbin gine-gine da shaguna masu Kayatarwa na zamani masu hawa uku suna kokarin kwashe kayayyakin dake cikin ginin.

Shaidu sun tabbatar da cewar, wasu daga cikin ‘yan kwangilar aikin sunyi saurin afkawa ciki da motoci domin kwashe ragowar kayayyakin su dake cikin shagunan bayan fitowar wata wasika da ake zargin an rubuta ta kan rushe ginin da akayi ba bisa ka’ida ba.

Duk da kasancewar tabbatuwar Jami’an tsaro a kofar shigar gidan Jaridar, matasan sun bankare babbar kofar ginin tare da fara cire kofofin shagunan da tagogi da sunan ganima.

Leave a Comment