Yanzu-Yanzu

Yanzu-Yanzu: Wasu Fulani Sun Kashe Mutane 2, Sun Cinye Amfanin Gonaki 50 a Minjibir

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Yahaya Sadisu Alkasim

Wasu mutane da ake zargin Fulani ne sun Kashe wasu Mutane 2 tare da cinye amfanin Gonaki sama da 50 a yankuna sama da 10 na Karamar hukumar Minjibir.

Rotannin sun bayyana cewa Babban baturen ‘yan sandan yankin ya Sha da kyar bayan da mutanen da ake zargin Fulani ne sunyi kokarin harbinsa da sauran mutanen da suka tunkare su.

Wakilinmu Yahaya Sadisu Alkasim da ya ziyarci gari a yammacin yau Litinin ya ganewa idanun sa yadda mutanen da ake zargin Fulani ne suka cinye amfanin Gonaki a garuruwa sama da 10 na yankin.

Mutane dai suncinye amfanin Gonakin tare kuma da yin barazanar Kashe duk wanda ya tanka musu.

Garuruwan da abin ya shafa sun hada da Kanya-Hore da Jama’ar Ladan da Zabainawa da Kunya da Dukuji da kuma sauran yankuna da dama a Karamar hukumar ta Minjibir.

Ku karanta: Gwamnatin Kano Za ta Nemi Tallafin Bankin Duniya Don Gina Dam-dam Uku

Da yake tattaunawa da wakilinmu Yahaya Sadisu Alkasim, Dagacin Kunya Maikudi Muhammad ya roki Gwamnatin jihar Kano da rundunar ‘yan sandan jihar Kano su kaimu dauki domin al’umma yankin na zaune cikin dar-dar.

Itama wata da tayi gudun tsira da rai wacce ta bayyana Sunan ta Asiya ta shaidawa wakilinmu cewa ta sha gudu kafin tsira da ranta.

To amma, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce bashi da masaniya dangane da lamarin, Amma yayi alkawarin tuntubar jami’an Yan sandan yankin da kuma yi wa Pyramid Radio Karin bayani.

Leave a Comment