Yanzu-Yanzu

Yanzu-Yanzu: Ecuador Ta Yi Nasara a Wasan Farko Na Kofin Duniya

Written by Pyramid FM Kano

Kungiyar Kwallon kafa ta kasar Ecuador tayi nasara akan kungiyar Kwallon kafa ta kasar Qatar a Wasan Farko na gasar cin Kofin Duniya da aka buga a kasar Qatar.

Qatar dai itace kasa ta Farko da ta taba karbar bakuncin gasar a yankin gabas ta Tsakiya, kuma karon Farko da take zuwa gasar cin Kofin Duniya.

Dan Wasan Ecuador E. Valencia ne ya zurawa kasar sa kwallaye 2 tun a zagayen Farko na Wasan, Kuma haka aka tashi Qatar na nema Ecuador na da 2.

To amma an sauya Valencia daga Wasan bayan yayi rauni a zagaye na biyu na Wasan.

Ku Karanta: Tsaftar Muhalli: Mun Sauya Tsarin Aiki Zuwa Duba Guraren Samar da Abinci ga Al’umma — Kabiru Getso

Alkalin Wasan Dan kasar Italy Daniel Osorto ne dai ya jagoranci wasan, kuma ya bayar da katin gargadi gudu 6.

Sai a gobe litinin ne za’a buga wasa na biyu a rukunin na A wanda kasar Senegal da Netherlands zasu buga da misalin karfe 5 agogon Nigeria.

Wannan ne dai karon Farko a tarihin gasar da kasar da take karbar bakuncin tayi rashin Nasara a Wasan Farko.

Leave a Comment