Yanzu-Yanzu

Yanda Kyakykyawan Shugabanci Ke Kawo Cigaban Al’umma A Kowanne Mataki – Michael E.

Written by Pyramid FM Kano

Daga: KABIR GETSO

Shugaban kungiyar Ma’aikatan jinya da unguwar zoma ta kasa “National Association of Nigeria Nurses and Midwives” (NANNM) Nnachi Michael E.
ya bayyanna cewa kyayyawan shugabanci da shuwagabanni nagari shi ke kawo nasarori da cigaban al’umma a kowanne mataki.

Michael E. wanda Ma’ajin Kungiyar ta kasa Comrade Lensy Laraba Linkha ta wakilta a taron ganawa da wakilan kungiyar ta NANNM reshen Jihar Kano domin zabar sabbin shuwagabanni inda ya gudana a harabar sakariyar kungiyar dake cikin Birnin Kano a yau Alhamis.

Comrade Laraba ta ce, babu shakka idan wakilai da mambobin kungiyoyin na jajircewa da tabbatar da gaskiya da rikon amana to ga wadanta take shugabanta babu shakka wadanda ake shugabanta zasu zamo masu amfanuwa da alfahari ga shugabancinsu.

Ta kara da cewar, shugaban kungiyar na Jihar Kano Comrade Ibrahim Maikarfi yayi abin a yaba a tsawon wa’adin shekaru 4 da suka gabata, domin bayanin da ya gabata na irin ayyukan da ya samar da irin gwagwarmayar da yayi ya nuna cewar lallai ya cancanci rike ko wanne irin mataki a kungiyance.

Laraba Linkha ta kara da cewar kunshin shugabancin kungiyar na Jihar Kano ana alfahari da shi a dukkanin kasar nan idan aka duba yadda tarihi ya nuna tun daga kafuwar kungiyar a shekaru da dama da suka gabata.

Kazalika, tayi kira ga sauran wakilan wannan Kungiya da su tabbatar sun zabi wanda ya dace a zaben da kungiyar zata gudanar a gobe Juma’a, domin cigaba da samun kyawawan tsare-tsare da zasu cigaba da ciyar da kungiyar gaba.

Shima a nasa jawabin, Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Abubakar Labaran Yusif wanda Darakta mai kula da jinya da unguwar zoma na Ma’aikatar lafiyar jihar Kano Dr. Jibrin Usaini Danbatta ya wakilta. Ya bayyanna gamsuwarsa da yadda kungiyar ke taimakawa a fannoni da dama, musamman samun hadin kai ga mambobi da samar da bita ta musamman da taimakwa Gwamnati wajen wayar da kan Ma’aikatan, inda yayi albishir da cewa Gwamnatin jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusif na nan tafe da kyawawan tsare tsare don inganta sha’ainin ayyukansu.

Shugaban kungiyar ta NANNM wanda kuma yake nema a karo na biyu Comrade Ibrahim MaiKarfi ya bayyanna irin nasarorin da ya samu, ya same su ne bisa cikakken hadin kan da Sauran ‘ya’yan Kungiyar ke bashi don haka yayi kira da wakilan da zasu gudanar da wannan zabe a gobe Juma’a da su kara bashi dama domin kara cigaba da gwagwarmayar fafutukar cigaban Ma’aikatan Jinya da unguwar Zoma na jihar Kano.

Mai karfi ya yabawa Gwamnaatin Jihar Kano bisa irin gudummuwar da take bawa Ma’aikatan Lafiya, inda yayi roko da ta rubanya kokarinta domin Ma’aikatan su samu sukunin aikinsu yadda ya kamata, ya kara da cewar abin takaici ne ace kwararrun Ma’aikatun lafiya na kwarara kasashen ketare duk da karancinsu da ake da shi a cikin kasar nan, wanda hakan na faruwa ne a sakamakon wasu matsaloli da suke rokon Gwamnatin ta shawo kansu.

Taron ya samu halartar Tsoffin Shuwagabanni Kungiyoyin kwadago da sauran manyan Daraktocin Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano.

Leave a Comment