Kasuwanci

‘Yan Kasuwa Sun Gamsu da baiwa Musbahu Mukaddashin Gwamna – Dangishiri

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar ‘yan kasuwa a nan jihar Kano, sun bayyana jin dadin su bisa baiwa Musbahu shadow matsayin maitaimakawa Gwamnan jihar Abba Labir Yusuf a bangaren harkokin kasuwanni.

Alh Mu’azu Dangishiri wanda shugaban gamayyar kungiyoyin ‘yan kasuwa ne ya tabbatar da haka a wata zantawa da manema labarai a ofishinsa dake Kasuwar Singa anan Kano.

Alh Mu’azu Dangishiri yace ko mutum baya son Gwamnan jihar ta Kano Abba Kabir Yusuf, yana da wasu abubuwa guda biyu, inda yace, Abba yana da biyayya da kuma, bibiya ga wadanda aka zalunta.

Yace, Gwamnan jihar Kano Abba, yayi mutukar hangen nesa da ya dauko Alh Musbahu Shadow ya bashi matsayin mai bashi shawara akan harkokin kasuwannin jihar Kano, wanda ya san zai taka rawar gani wajen bunkasar ci gaban kasuwanci a fadin jihar.

Dangishiri yace, lokaci yayi da kasuwanci zai samu tagomashi na musamman domin Shadow, mutum ne da yake da nagarta da sadaukar da kai wajen taimakawa Al’umma, inda yace, yin hakan zai taimaka gaya wajen sauke nauyin da Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya dora masa na kulawa da harkokin kasuwanci a fadin jihar Kano.

A jawabinsa daya daga cikin Dattawan shugabannin dake kula da al’amuran gamayyar kungiyoyin ‘yan kasuwa a fadin jihar Kano, Alh. Bukar Iliyasu Dan Marafan Dan Majen Kamo, ya bukaci kungiyoyin ‘yan kasuwa a jihar Kano, da su baiwa tsarin da Gwamnati ta bijiro da shi, na yin rijista da ma’aikatar harkokin kasuwanci, wanda yace, yin haka zai taimakawa ‘yan kasuwa wajen ci gaban kasuwancinsu da kuma, bunkasa tattalin arzikin kasuwanci.

Marafan Danmajen Kano, ya bayyana gamsuwarsa bisa wannan tsari wanda yace, wannan abune da zai haifar da ‘Da mai ido a fannin harkokin kasuwanci.

Alh. Bukar iliyasu, yace, ‘yan kasuwar Singa a shirye suke wajen ci gaba da baiwa Gwamnatin jihar Kano goyan bayan da suka kamata wajen ganin an ciyar da kudirin Gwamnatin jihar kano, musamman a bangaren harkokin kasuwanci.

Leave a Comment