Labaran Kasa

“Yan Jaridu Ku Himmatu Domin Jan Hankàlin Gwamnati Halin Da Al’umma Ke Ciki Dangane Da Tsaro – Bello

Written by Pyramid FM Kano

Daga: KABIR GETSO

Wani babban Dan Kasuwar Canji a babban birnin tarayya Abuja Alh. Bello Zamfara yayi kira ga manema labarai da su kara himma wajen ankarar da mahunkunta halin da al’umma ke ciki game da tsaro.

Alh. Bello ya bayyyana hakan ne lokacin da yake ganawa da wakilan Kungiyar ‘Yan Jaridu masu binciken Kwakwaf (Arewa Investigative journalists’s) a Ofishinsa dake Abuja, yace babu shakka jami’an tsaro na iyakar kokarinsu wajen yaki da matsalar Tsaro amma akwai rawar da ‘yan Jaridu zasu taka wajen taimakawa Gwamnati don kara fahimtar ta ita halin da al’umma ke ciki a wasu yankunan.

Ya kara da cewar garuruwa da dama al’ummar yankin na cikin firgici ta yadda ko samun damar yin noma babu domin gujewa abinda ka iya zuwa ya dawo, àwasu garuruwan kuma kiwo na gagarar makiyaya saboda barazanar ta tsaro. Don haka ya kamata al’ummar yankin da abin ya shafa su rinka kokari sanar da manema labarai domin sanar da Hukuma don kawo masu dauki na gaggawa

Jihar Zamfara da Katsina da Neja na cikin jihoshin da barazanar tsaro yafi ta’azzara a wannan lokaci, inda kullum al’ummar yankunan ke neman dauki daga Mahunkunta.

wajibi ne a yabawa Jami’an Bijilanti da na Sakai bisa irin gagarumar gudummuwa da suke bayarwa wajen tabbatar da tsaro, don haka ya Kamata Gwamnati ta rubanya kokarinta na basu kulawar da ta kamata domin basu kwarin Gwiwar wannan aiki da suke

Aikin Jarida aiki ne mai matukar tasiri ga rayuwar al’umma don haka abu ne mai kyau “Yan Jaridu su cigaba da jajurcewa don taimakawa al’umma domin samun saukin rayuwar da suke ciki.

Suma masu hannu da shuni su cigaba da kokari na taimakawa Mabukata a wannan yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa wanda hakan ke kara haifar da zaman lafiya da kaunar juna ga marasa galihu da kuma masu hannu da shuni.

Alh Bello yayi kira ga sauran al’ummar kasar nan da aci gaba da addu’a da neman yafiyar Allah domin samun saukin wannan yanayi da al’umma ke ciki.

Leave a Comment