Labaran Kasa

‘Yan bindiga sun kai hari cibiyar POS a Bauchi

Written by Pyramid FM Kano

Mutane hudu sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga bayan wani hari da aka kai a cibiyar gudanar da ayyuka ta POS da ke karamar hukumar Zaki a jihar Bauchi.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai farmakin ne a wurin ajiye motoci inda suka sace kusan Naira miliyan 7 mallakar ma’aikacin POS da kwastomomi.

Gwamnan jihar, Bala Mohammed yayin da yake jajantawa wadanda lamarin ya shafa da aka kwantar a cibiyar kula da lafiya ta tarayya Azare, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

A wani labarin kuma Gwamna Mohammed ya duba irin barnar da aka yi a sakamakon fashewar wani abu mai kama da bama-bamai a wani shago da ke karamar hukumar Katagum wanda ya lalata wani masallaci da wani yanki na wani gida da kaddarori.

Ya sanar da bayar da gudunmuwar ga wadanda fashi da makami ya rutsa da su, tare da biya musu kudaden jinya sannan ya kuma bukaci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA da ta dauki nauyin irin barnar da fashewar ta haddasa domin baiwa gwamnati damar kai dauki.

Da yake karin haske ga Gwamnan, kwamishinan ‘yan sandan jihar Aminu Alhassan ya ce an kama mutum guda da laifin fashi da makami.

Leave a Comment