Lafiya

Yaki Da Tarin-Fuka: Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Kano Za Su Yi Aikin Hadin Gwiwa

Written by Pyramid FM Kano

By: Muktar Yahaya Shehu

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta yi Aikin Hadin Gwiwa da Gwamnatin Tarayya domin yaki da cutar tarin Fuka.

Kwamishinan lafiya na jiha Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya sanar da haka yayin kaddamar da wasu Babura masu kafa Uku na tafi-da-gidanka domin gwajin cutar Tarin-fuka da gwamnatin tarayya ta Samar a nan Kano.

Ya ce abin alkairi da gwamnatin tarayya ta yi abin a yaba ne kuma ya zo dai dai da kudurin gwamnatin jihar Kano a sha’anin bai wa fannin lafiya kulawar da ta dace.

Aminu Tsanyawa ya ba da tabbacin ganin an yi amfani da su ta hanyar da ta dace, tare da bukatar samun karin na’urori na musamman domin samar wa a dukkanin manyan masarautun jihar guda biyar.

Ku karanta: Za Mu Cigaba Da Bada Gagarumar Gudun Mowa a Bangaren Lafiya — Aminu Ado

Da ya ke Karin haske, Dakta Ibrahim Aliyu Umar shugaban sashin yaki da cutar Tarin-fuka a ma’aikatar lafiya ta jiha ya ce an samar da na’urori ta hanyar Babura masu kafa Uku domin shiga lungu da sako domin gwajin cutar da Kuma fara dora mara lafiya kan magani idan an tabbatar yana dauke da cutar.

Ibrahim Umar ya ce na’urorin na gwajin cutar ta hanyar amfani da Babura masu kafa Uku gwamnatin tarayya ta samar da guda biyar ne a duk fadin kasar nan Wanda Kuma aka bai wa jihar Kano guda biyu ne bisa la’akari da yadda ta ke tallafawa sha’anin lafiya a jihar.

Ya Kara da cewa baya ga gwajin cutar Tarin-fuka, na’urorin suna yin gwajin cututtukan suga da hawan jini nan take.

Leave a Comment