Addini Lafiya

Ya Kamata Mutane Su Bayar Da Muhimmanci Kan Gwajin Jini Kafin Aure.

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar dake wayar da Kan al’umma dangane da yin gwaji kafin aure ta jihar Kano, ta Sha alwashin ci gaba da wayar da kan matasa maza da mata mahimmancin gwaji kafin aure domin samun ‘ya ‘ya masu koshin lafiya.

Shugaban kungiyar na jihar Kano Alhaji Muharazu Adamu ibrahim Gizina ne, ya ba da tabbacin hakan a lokacin da kungiyar ta ziyarci makarantun sakandiren yan mata ta Yakasai dake birnin Kano da kuma, ta Dorayi dake karamar hukumar Gwale domin ci gaba da wayar da Kan matasa amfanin yin gwaji kafin aure, domin kaucewa haifar Yara masu dauke da cutar amosanin jini da sauran cututtuka.

Muharazu Adamu ya ce, kungiyar an kafata ne, karkashin jagorancin matasa masu kishin alummar jihar Kano da Najeriya, kasancewar iyaye suna mutukar shan wahalar kashe kudi da dawauniya idan suka samu Yara masu dauke da cutar amosanin jini.

Ku karanta: Amosanin-Jini: Za Mu Tallafawa Masu Cutar Ta Kowacce Hanya — Sarkin Kano

Shugaban kungiyar ya bukaci gwamnatin tarayya da ta jiha da sauran shugabanni masu rike da masarautun gargajiya da su taimakawa yunkurin kungiyar na ci gaba da wayar da kan matasa maza da mata amfanin yin gwaji kafin aure domin kaucewa samun yara marasa koshin lafiya.

A jawabinsa, mataimakin shugabar makarantar yan mata dake unguwar Yakasai, Malam Sadik Tijjani, ya nuna farin cikinsa bisa ziyarar wayar da kan matasa amfanin yin gwaji kafin aure domin Mata sune wadanda ya kamata a wayarwa Kai domin kaucewa fadawa cikin irin wannan yanayi.

Itama a nata jawabin, shugabar makarantar yan mata ta Dorayi dake karamar hukumar Gwale, Halima Imam, ta jaddada aniyarta na baiwa shugabancin kungiyar goyan bayan daya dace domin samun damar cin nasarorin da aka Sanya a gaba a gaba, na wayar da Kan matasa maza da mata amfanin yin gwaji kafin aure.

Ku karanta: Ku Tabbatar Da Gwajin Jini Kafin Daura Aure, Hakimin Ajingi Ga Limamai

Daga karshe ta shawarci iyaye da su kasance masu kulawa da lafiyar wadanda suka zo domin neman Auren yayansu duba da wahalar dake tattare da cutar amosanin jini da sauran cututtuka da ake kamuwa da su ta hanyar auratayya.

Leave a Comment