Yanzu-Yanzu

Wata Kungiya ta Bukaci Jam’iyyar APC da ta janye Batun Zaben Shiyya a Shugabancin Majalisar Dattawa – Aminu

 

By: KABIR GETSO.

 

Shugaban Kungiyar Alhaji Aminu Adam ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da suka gudanar a Haitel Hotel a ranar Lahadi a Birnin Kano.

Alhaji Aminu Adam ya ce babu shakka Sanata Barau Maliya ya cancanci zama shugaban majalissar domin za a ajiye kwarya ce a gurbinta, dan samalwa al’ummar Najeriya mafita daga halin da Kasar ta ke ciki.
Ya kara da cewa, Sanata Barau yana da kyakkyawar alaka tsakanin sa da zababben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, wanda hakan zai taimaka wajen kawo ci gaba ga yan kasa Najeriya.
Shugaban kungiyar Barau Maliya Support Network Aminu Adam, ya zaiyano wasu daga cikin kalubalen dake kawo rashin fahimta dake tsakanin shugaban kasa da kuma shugaban majalissar Dattawa, wanda hakan yake samarwa, dimokuradiyya tasgaro wajen samar da aiyukan ci gaba ga al’umma.
Kungiyar ta misalta yadda shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya sami rashin fahimta da tsohon shugaban majalissar Dattawa, Ken Nnamani, haka zalika shima tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya fuskanci irin wannan matsala.
Ya kara da cewa hatta shugaban kasa mai barin gado Muhammadu Buhari ya fuskanci irin wannan matsala daga tsohon shugaban majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki a majalissa ta 8.

‘’Haka nan kuma, domin samar da Damokoradiyya mai inganci akwai bukatar samun shugabancin majalisar da ba zai zama dan amshin shatar shugaban kasa ba, akan harkokin mulkin da ba zai cutar da al’ummar kasa ba, Aminu Adam’’.

Kungiyar ta ce, Barau Maliya yana majalisa tun haihuwar dimokoradiyya a Najeriya har zuwa yanzu babu wanda yake da kalubalantarsa sakamakon gazawa a aiyukan samar da ci gaban al’ummarsa tun a 1999 shi ne shugaban kwamitin makamashi a majalisar tarayya, mafi kyawun abunda sanatoci 108 za su zabi Sanata Barau damar zama shugaban majalisar dattawa.

A karshe kungiyar Barau Maliya Support Network, ta yi kira ga uwar jam’iyar APC ta kasa data kau da maganar shiyya-shiyya a yayin zaben cancanta.

Leave a Comment