Labaran Jiha

Wani Hakimi Yayi Kiran Mahukuntan Kan Yiwuwar Dawo Da Makaranta Kwana A Kano

Written by Admin

Anyi kira ga gwamnatin jihar kano kan ta duba yiwuwar farfado da makarantun kwana a jihar.

Kiran ya fito daga bakin Hakimin Albasu AIG. Alh. Mu’azu Abubakar Gagarami. a wajen taron sada zumuncin da tsofaffin daliban makarantar sakandire ta Albasu suka shirya da niyyar ganawa da fuskokin juna.

A nasa jawabin, Kwamishinan ilmi na jihar Kano Hon. Umar Haruna Dogowa wanda ta bakin wakiliyarsa yace, tabbas gwamnati zata bude makarantun kwanan duba da yanda jihar Kano ta samu cikakken tsaro a halin yanzu.

Anata bangaren, shugabar kungiyar tsofaffin daliban ta Albasu tace, babban burinsu a wannan tafiya hadin kai kasancewar wannan shine Karo na farko da suka shirya irin wannan taro.

Ayayin wannan taro, an gabatar da shaidar girmamawa ga kafatanin tsofaffi da sabbin Malaman Makarantar tare da shuwagabannin makarantar.

Taron dai, ya gudana ne a dakin taro na Trade Fair dake kan TITIN GIDAN ZOO wanda ya samu halattar manyan bakin ciki da wajen jihar Kano.

Leave a Comment