Da Dumi-Dumi

Yanda Muke Inganta Hukumar Yawon Shakatawa – Ladidi Garko

Written by Pyramid FM Kano

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar ikano ta sha alwashin dawo da martabar harkokin yawon shakatawa da raya al’adu domin bunkasa tattalin arzikin jihar nan.

Kwamishiniyar ma’aikatar yawon shakatawa da raya al’adu ta jihar Kano Hajiya Ladidi Ibrahim Garko ce ta furta hakan a taron masu ruwa da tsaki kan sha’anin yawon shakatawa irin sa na farko da aka taba yi a tarihin kafuwar hukumar wanda ya gudana a nan Kano.

Garko ta bayyana cewar an kirkiri ma’aikatarta shekaru hudu da suka gabata kuma ta riski ma’aikatar acikin mummunan hali ta yadda gurin zama ma ya gagari ma’aikatansu sai a karkashin bishiya suke zama.

Ta kuma bayyana cewar a ranar da ta kama aiki a ma’aikatar a ranar ta karbi takardar kama aiki kuma a ranar ta karbi kudadenta don haka a yanzu duk wanda ya shiga ma’aikatar zai tabbatar wa idanunsa cewar an samu sauyi mai yawan gaske.

Kwamishiniyar ta kuma yabawa Manajan Darakta na hukumar da kuma na hukumar kula da dabbobin daji bisa kokarinsu wajen farfado da hukumominsu domin su dawo cikin hayyacinsu sabanin yadda suke a shekarun baya.

Shima anasa jawabin Manajan Darakta na hukumar kula da yawon shakatawa na jihar Kano Alhaji Tukur Bala Sagagi ya bayyana farin cikinsa bisa wannan taro Wanda baa taba yin sa ba tun farkon kafuwar hukumar sai wannan karon kuma an samu nasarar da ake da bukata.

Sagagi yace makasudin shirya wannan taro shine wayar da mutane muhimmancin karramawa da yawon shakatawa da kuma lalubo hanyoyin da zaa tattauna matsaloin da suka addabi harkokin yawon shakatawa da Kuma magance su.

Ya kara da cewar gwamnan jihar Kano Alhaji Abba kabir yusuf yayi musu alkawarin cewa yana so ya kafa tarihi abin koyi a maaikatar kuma yana neman hadin kansu da goyon bayansu domin cimma wannan burin.

Leave a Comment