Da Dumi-Dumi

Wajibi a Kauracewa Gudun Wuce Sa’a

Written by Pyramid FM Kano

By: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar matuka manyan motocin haya dake kasuwar Tafawa Balewa ta bukaci direbobin manya motoci na unguwar Tafawa Balewa da su kasance masu bin dokokin hanya, musamman su da suke bin manyan hanyoyin kudu da arewacin kasar nan.

Shugaban sashin kula da harkokin sufuri na kungiyar Alhaji Haliru Ibrahim Gizina ne ya bukaci hakan a lokacin da yake zantawa manema labarai a ofishinsa dake Tafawa Balewa anan jihar Kano.

Haliru Ibrahim Gizina yace, ba wai sai lokacin hunturu ba za’a ja hankalin direbobi ba kan su rika kiyayewa da umarnin hukumomi masu kula hanyoyi da kaucewa gudun ganganci inda yace, shugaban A.A Gizina, ya himmatu wajen ganin an inganta harkokin tuki da hakkokin direbobin dake safara zuwa jihohin Kudu da Arewacin Najeriya.

Haliru Gizina, yayi kira ga matuka manyan motoci su tabbatar suna bin dokoki da ka’idoji yadda suka kamata domin kaucewa afkuwar hadura.

Yace, kamata yayi direbobi su zamto masu bin dukkannin dokokin da aka gindaya musu domin samun nasarar da aka sanya a gaba na ciyar da harkokin sufurin manyan motoci ta yadda jihar Kano za ta yi gogayya da sauran jihohin kasar nan.

Haka zalika, ya bayyana cewa, wannan lokaci ne daya kamata duk wani direba ya kasance masu kulawa a lokuta daban daban, ba ma sai an Shawarce su ba,su kiyaye dokokin da aka sanya akan al’amuran da suka shafi tuki.

Haliru Gizina ya yabawa gwamnatoci a matakai daban -daban da hukumomin dake lura da harkokin tuki bisa jajircewa da suke yi wajen wayar da kan direbobi domin ciyar da al’amuran da suka shafi sufuri.

Yace, kungiyar direbobin manyan motoci ta Tafawa Balewa za ta ci gaba da baiwa gwamnatoci da hukumomin cikakken hadin yadda ya kamata domin bunkasar harkokin sufuri a jihar Kano da ma kasa baki daya.

 

Leave a Comment