Muhalli

Tsaftar Muhalli: Mun Sauya Tsarin Aiki Zuwa Duba Guraren Samar da Abinci ga Al’umma — Kabiru Getso

Written by Pyramid FM Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta sauya tsarin kula da Muhalli na kasuwanni da maaikatu harma da hukumomin gwamnati zuwa gurare da kasuwannin samar da abinci ga al’umma domin tabbatar da kula da lafiyarsu.

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan bayan kammala tsaftar Muhalli ta kasuwannin da maaikatun da guraren sana’a harma da hukumomin gwamnati wacce ake gudanarwa a duk juma’ar karshen wata a nan Kano.

Kwamishinan ya ce sun dauki matakin ne domin tabbatar da tsaftar kayayyakin da ake siyarwa al’umma wanda hakan zai bada gudun mowar wajen kula da lafiyar su.

A yayin tsaftar Muhalli, an ziyarci kasuwannin uku da suka hadar da Kasuwar Galadima da Kasuwar Nama (Abbatuwa) da kuma Kasuwar Rimi, inda kwamishinan ya yabawa kasuwar galadima musamman guraren da ake sayar da kifi da kuma Mai na abinci, yana mai cewa sun kula da tsaftar kayayyakin da suke sayarwa da mutane.

“Kasancewar kasuwar galadima ana siyar da kifi da man girki, abubuwa masu sauran lalacewa, amma mun yaba kan yadda ma’aikatan mu da Yan wannan kasuwa sukayi aiki tare aka tabbatar da tsaftar wannan kasuwa, Gaskiya munji dadi kuma mun yaba musu sosai, akwai inda muka ga gyare-gyare musamman ma bandakunan su, kuma mun gaya musu a tabbatar an gyara wannan guri yayi da suka bamu tabbacin aiwatar da gyaran, sannan kuma kwatar da take gaban gurin an yashe ta domin inganta tsaftar gurin, amma idan aka duba gaba daya mun gamsu da yadda sukayi aikin, kuma sun cancanci a yaba musu”, inji Getso.

Ku Karanta: Tsaftar Muhalli: An ci Tarar Tashar Motar Rijiyar Zaki Dubu 100, Kowacce Mota Dubu 10

Daka Kabiru Getso ya kuma bayyana jindadin sa da gamsuwa da yadda shugabanni da Yan kasuwar Abbatuwa suke kula da tsaftar Naman da su ke siyarwa al’umma yana mai cewa Gwamnatin jihar Kano karkashin ma’aikatar Muhalli zata rubuta musu lambar yabo ta kuma aike musu da ita, a matsayin wani bangare na yabawar bisa yadda suke kula da tsafta da lafiyar naman da suke sayarwa mutane.

Ya ce “abin a yaba ne yadda suke kula gami da tabbatar da cewa sai dabba Mai lafiya za’a yanka, kuma idan an yanka akwai jami’an lafiya da dakin gwaji a kasuwar ta yadda idan nama yana da cutar za’a ware shi kuma a lalata shi, mun gani suna da asibiti da maaikata, yadda za’a duba dabbar kafin a yanka, kuma idan an yanka za’a sake dubawa a tabbatar lafiyar ta kalau don munga har wani Naman da bayan an yanka shi aka gano wani bangare nasa ya lalace kuma aka ware shi za’a lalata shi, sannan mun duba gurin da ake yanka dabbobin munga yadda akayi daben gurin, an saka tarazo ta yadda baza a rika samun matsala ba, sannan kuma munga ishashshen ruwa a gurin, Gaskiya mun yaba sosai kuma zamu rubuta musu lambar yabo amadadin gwamnatin jihar Kano”.

Kwamishinan ya kuma yabawa shugabanni da Yan kasuwar Rimi dake nan Kano bisa yadda suke kula da tsaftar Muhallin su.

Ku Karanta:Zamu Kashe Miliyan 70 a Fadada Magudanan ruwan Shataletalen Baban Gwari — Kabiru Getso

Ya ce akwai rufin dakin wata Karamar mayanka a kasuwar da aka gano gyare-gyare a cikin kuma an basu gyaran domin tabbatar da kula da rayuka da kuma lafiyarsu.

Dakta Kabiru Getso daga nan ya bukaci iyaye da ja kunnen yayan su, da su guji yi wasanni Musamman kwallon kafa lokacin da ake tsaftar Muhallin yana Mai cewa an tanadi kotun tafi-da-gidan ka domin hukunta duk wanda aka samu da laifin karya dokar.

A jawabinsa, shugaban kasuwar Rimi dake nan Kano Alhaji Salisu Ya’u Yola ya bayyana farin cikin sa dangane da ziyarar, daga nan ya bada tabbacin cigaba da kula da tsaftar Muhalli.

Ya ce mafi yawan kayayyakin da suke siyarwa na amfanin yau da kullum na abinci kuma zasu cigaba da gudanar da ayyukan tsaftar Muhalli a Koda yaushe.

Leave a Comment