Da Dumi-Dumi

Tsaftar Muhalli: Kotu Ta Yiwa Tashar Kano Line Tarar 200,000

Written by Admin

Daga: SANI MAGAJI GARKO 

Kotun tafi da gidan ka ta kwamitin koli na tsaftar muhalli na jihar Kano ta yiwa tashar Motar Kano Line tarar naira dubu dari biyu (200,000).

Kotun karkashin jagorancin majistire Auwal Yusuf Suleiman ta sami tashar da lefin karya dokar tsaftar muhalli wanda hakan ya sa aka yi musu tarar.

A lokacin da kwamitin yake zagayen duba aikin tsaftar muhallin, ya tsaya a bakin tashar sakamakon ganowar da akayi suna lodi zuwa garuruwa lamarin da ya ci karo da dokar tsaftar muhalli.

Da yake karantawa shugabannin tashar hukuncin Kotun, Majistire Auwal Suleiman ya ce bayan samun su da lefi kotu tayi musu tara.

“Sakamakon samun ku kuna yin lodi a lokacin tsaftar muhalli kuma gwamnati da sanya doka cewa wannan lokacin na tsaftar muhalli ne, saboda haka kotu ta yiwa dukkan tashar tarar naira dubu dari biyu (200,000).”

A wani cigaban labarin kuma Kotun ta yiwa wasu direbobi biyu tarar naira dubu goma (10,000) kowannen su.

Kotun ta same su ne suna lodi a haramtacciyar tashar mota dake karkashin (Ado Bayero Bridge) wacce akafi sani da gadar Lado.

Leave a Comment