Muhalli

Tsaftar Muhalli:  Gwamnatin Kano Ta Bawa Tashar Motar Kano Line Wa’adin Kwanaki Biyu Ko Ta Dauki Mataki

Written by Pyramid FM Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bawa shugabanni tashar Motar Kano Line Wa’adin kwanaki biyu da su tsaftace tashar ko kuma ta dauki mataki akan su.

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan lokacin tsaftar Muhalli ta kasuwanni da tashoshin Mota da Guraren Kasuwanci da maaikatu harma da hukumomin gwamnati da ake gudanarwa a duk juma’ar karshen wata a nan Kano.

Dakta Kabiru Getso ya ce abin takaici ne yadda tashar Motar ta kasance cikin Datti da Ledoji da shara wanda hakan ka iya taimakawa wajen yaduwar cututtuka ga matafiya da masu gudanar da harkokin su a tashar.

Kwamishinan ya kuma umarci shugabanni tashi da su tabbatar an daina zubar da shara a jikin katangar tashar wacce ta hada ta da sakatariyar Audu Bako, yana mai cewa ma’aikatar Muhalli zata ajiye Bokitin zuba shara a gurin wanda da zarar ya cika jami’an ma’aikatar zasu dauke.

Ku Karanta: TSAFTAR MUHALLI: Gwamnatin Kano Ta Bawa Kasuwar ‘Yan-lemo Wa’adin Kwanaki Uku

Haka Kuma, kwamishinan ya bayyana takaicinsa bisa yadda ‘Yan Kasuwar Kwari a yankin karamar hukumar Birnin Kano suke zubar da shara a tsakiyar titi wanda hakan ke Maida hanun agogo baya akokarin da ma’aikatar ta ke yi na tsaftace birnin Kano da kewaye.

A cewar kwamishinan “Kasuwar kantin Kwari munje ne saboda yadda Yan wannan kasuwa suke zuba mana shara akan titi, a wannan tsaftar Muhalli ta mu ta jumaar karshen wata mun fito da wani tsari ta yadda zamu rika duba guraren da muke da matsaloli, saboda haka munje wannan kasuwa, mun zagaya da shugaban kasuwar ta Kwari yaga dukkan wadannan matsaloli kuma mun tattauna kan yadda za’a shawo kansu domin Kara inganta tsaftar wannan kasuwa Baki daya kuma sun bamu tabbacin aiwatar da tsare-tsaren duba da cewa kullum sai mun tura motoci da babura masu kafa uka da Tractor domin kwashe sharar”.

Dakta Kabiru Getso ya kuma jagoranci kwamitin koli na tsaftar Muhalli na jihar Kano inda suka ziyarci kasuwar ‘Yan Katako ta Na’ibawa a Karamar hukumar Kumbotso inda ya yaba bisa yadda suke tsaftar Muhalli a kasuwar tare da bukatar su da su hada hanu da Gwamnatin jihar Kano domin inganta tsaftar kasuwar.

Ku Karanta: Tsaftar Muhalli: An ci Tarar Tashar Motar Rijiyar Zaki Dubu 100, Kowacce Mota Dubu 10

“Gwamnati ta sayi wani Fili da ake zuba shara a ciki, to Amma kasancewar gurin kasuwa ce da mutane suke hada-hada ta kasuwanci dole ne shugabanni kasuwar su hada hanu da ma’aikatar Muhalli don a rika debe dukkan diddigar Katakon da aka yanka a kasuwar da kuma inganta tsaftar Muhalli”, inji Getso.

A jawabinsa, Santa ofisa na Tashar motar Kano line Abdu Sarki Mai-sango ya yabawa ma’aikatar Muhalli bisa ziyarar da ta Kai kasuwar wanda a cewarsa da ta tallafa musu wajen tabbatar da tsaftar Muhalli.

Abdu Sarki ya bada tabbacin aiwatar da dukkan gyare-gyaren da aka basu tare da yin alkawarin kulawa da Bokitin da Gwamnatin jihar Kano zata ajiye idan aka debe sharar gurin.

Leave a Comment